Dubu ta Cika: Sojoji Sun Kwamushe Rikakken Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri a Arewa

Dubu ta Cika: Sojoji Sun Kwamushe Rikakken Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri a Arewa

  • Dakarun sojin Najeriya sun yi ajalin wani kasurgumin mai hada kai da ‘yan ta’adda a yankunan jihar Kaduna a Arewa maso Yamma
  • Rahoto ya bayyana cewa, yanzu haka an kama wasu yaransa guda shida, kuma an zarce dasu sansanin soji
  • Ana yawan samun hare-hare da barnar ‘yan bindiga a yankunan Arewa maso Yamma, musamman Kaduna

Kagarko, jihar Kaduna - Dakarun sojin Najeriya sun hallaka rikakken mai kai wa ‘yan bindiga bayanan sirri, Malam Goma a maboyarsa da ke Kagarko a jihar Kaduna.

Wani mazaunin yankin, Shehu Bala ne ya bayyana hakan, inda yace farmakin na soji ya faru ne a ranar Alhamis din da ta gabata a lokacin da sojojin suka zo garin Kagarko tare da lallasa tsageru.

Rundunar Sojin Najeriya
Rundunar Sojojin Najeriya. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa, mai kai wa ‘yan bindiga bayanan ya yi kokarin tserewa a lokacin da ya ga dakarun soji, amma dubunsa ta cika aka yi ram dashi, suka saka shi a mota kana suka bude masa wuta, cewar jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yanayin Shigar Rahama Sadau Zuwa Wajen Bikin Karrama Yan Fim Ya Bar Baya Da Kura

Ya kara da cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A zahirin gaskiya, tuni an ayyana neman wanda ake zargin ruwa a jallo na tsawon lokaci bisa zarginsa da sace-sacen mutane a yankunan Kagarko da kauyukan makwabta.”

An kama yaransa 6, an zarce dasu sansanin soji

Politics Nigeria ta tattaro cewa an kuma kwamushe wasu mutum shida da ake zargin yara ne ga kasurgumin mai hada kai da ‘yan ta’addan.

Ya zuwa yanzu, rahoto ya ce sojojin sun tafi dasu sansaninsu, inda daga nan ne za a dauki mataki na gaba da ya dace.

Rundunar 'yan sandan ba ta ce komai ba game da harin

A bangaren ‘yan sanda, an nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, amma bai amsa waya ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Sojoji Sun Cafke Wani Basarake Mai Hada Baki Da 'Yan Bindiga a Kaduna

A wani labarin, rundunar sojojin Najeriya sun kai samame kauyen Janjala tare da cafke barasaken da ake zargi da bai wa 'yan bindiga bayanan sirri a karamar Kagarko da ke jihar Kaduna,

An kama Basaraken mai suna Mallam Ibrahim Aliyu da wasu mutane 13 masu bai wa 'yan bindiga bayanai

Asali: Legit.ng

Online view pixel