Dan Takarar Sanatan NNPP a Jihar Nasarawa Ya Sha Da Kyar a Yunkurin Halaka Shi

Dan Takarar Sanatan NNPP a Jihar Nasarawa Ya Sha Da Kyar a Yunkurin Halaka Shi

  • Ɗan takarar sanatan jam'iyyar NNPP a jihar Nasarawa ya tsallake rijiya da baya bayan an yi yunƙurin ɗaukar ransa
  • Dr Wakili Kabir-Muhammad ya tsallake rijiya da bayan ne bayan ƴan bindigan sun bi har gida sun yi yunƙurin halaka shi
  • Ɗan takarar sanatan ya bayyana cewa akwai waɗanda ake zargi kuma ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da hukumomi sun yi bincike

Jihar Nasarawa - Ɗan takarar sanatan Nasarawa ta Yamma a jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a zaɓen 2023, Dr Wakili Kabir-Muhammad, ya tsallake rijiya da baya a yunƙurin halaka shi da ƴan bindiga suka yi.

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa, ƴan bindigan sun dira cikin gidansa da ke a GRA cikin ƙaramar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa a ƙarshen makon da ya wuce.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari a Jihar Benue, Sun Salwantar Da Rayukan Mutane Da Dama

'Yan bindiga sun yi yunkurin halaka dan takarar sanatan NNPP
Dan takarar sanatan ya sha da kyar a harin da aka kai masa Hoto: Guardian.com
Asali: UGC

Ɗan takarar sanatan ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar nasarar Ahmed Wadada a zaɓen sanatan Nasarawa ta Yamma, a zaɓen 2023, cewar rahoton Sahara Reporters.

Yana zargin wasu ne ke ƙoƙarin ganin bayansa

Da ya ke zantawa da manema labarai kan lamarin a ranar Litinin, a birnin Lafia, Kabir-Muhammad, wanda ya ce harin yana da alaƙa da siyasa, ya ce ya kai rahoton lamarin gaban ƴan sandan ƙaramar hukumar Keffi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Ina so in bayyana abinda ya faru a matsayin mai fuska biyu, ɗaya siyasa ce, yayin da ɗayan kuma ba zai faɗu yanzu ba, wanda ni kaɗai na san da shi. Tabbas mu na zargin wasu abokan kasuwancin mu da siyasa."
"A bayyana ya ke na tsallake mutuwa ranar Lahadi, saboda ƴan bindigan a shirye suka zo, kamar yadda iyalaina da suka tarar suka gayamin, sun yi musu barazanar kisa idan basu bayyana inda na ke ba."

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Asalin Dalilin da Ya Sa Bola Tinubu Ya Gana da Kwankwaso a Faransa Ya Bayyana

"An gaya min cewa huɗu daga cikinsu sun kutsa cikin gidana ɗauke da AK-47 guda uku da ƙaramar bindiga ɗaya. Ni suka yi niyyar samu saboda sun yi ta tambayar ina na ke, an gaya musu cewa na je taro tare da matata, inda suka yi ta yi wa iyalaina barazana.
"Mafi yawan matsalolin sun taso ne daga siyasa, sannan za mu binciki wannan lamarin sosai ta hannun hukumomin da suka dace.

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa hedikwatar rundunar ba ta samu wani bayani ba dangane da lamarin.

Ƴan Bindiga Sun Halaka Bayin Allah a Kaduna

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun halaka wasu ƴan'uwan juna su biyu a ƙauyen Azara na jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da shanu 1,000 a wani ƙauye da ke maƙwabtaka da Azara a cikin jihar ta Kaduna.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Zabe Ta Yi Fatali Da Wata Bukatar Atiku da Peter Obi

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel