Yan Bindiga Sun Sheke Basarake Tare Da Kone Gawarsa a Cikin Mota

Yan Bindiga Sun Sheke Basarake Tare Da Kone Gawarsa a Cikin Mota

  • ‘Yan bindiga sun bindige wani mai sarautar gargajiya na Orsu Obota a karamar hukumar Oguta ta jihar Imo
  • An yi kisan ne a yankin Isama da ke gundumar Mgbele duk a cikin karamar hukumar Oguta
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya fadawa manama labarai cewa bai samu bayanai akan harin ba

Jihar Imo - ‘Yan bindiga sun hallaka wani mai sarautar gargajiya na Orsu Obota, Eze Victor Ijioma a karamar hukumar Oguta da ke jihar Imo.

Marigayin basarake gargajiyan an kashe shi ne a yankin Isama da ke gundumar Mgbele a karamar hukumar.

Jihar Imo
Jihar Imo na Fama da Hare-haren Yan Bindiga. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa masu sarautar gargajiya biyu ne aka kashe a hare-hare daban-daban a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu.

Rahotanni sun tabbatar cewa maharan sun tare marigayin ne a kwanar Umuamaka kusa da garin Izombe suka kashe shi a cikin motarsa kuma suka cinnawa gawarsa wuta.

Kara karanta wannan

Tsohon Sojan Amurka Ya Shiga Hannu Kan Zargin Shigo Da Makamai Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An sake kashe wani mai sarautar gargajiya

A wani labarin, an kuma kashe wani mai sarautar gargjiya na Mgbele wanda ba a ambaci ainihin sunansa ba a cikin garin.

Wata majiya ta tabbatar an samu karin jami’an tsaro a garin Izombe da Mgbele da kuma sauran yankunan da ke kusa da su a karamar hukumar Oguta saboda kokarin kamo wadanda suka aikata wannan kisan gillar.

Mazauna yankunan sun tsere daga gidajensu

Mazauna wadannan yankuna guda biyu sun tsere daga gidajensu saboda tsoron faruwar wasu hare-haren.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Henry Okoye ya bayyana wa manema labarai cewa har zuwa lokacin tattara wannan rahoto bai samu wasu bayanai akan kisan da aka yi ba.

Harin 'yan bindiga kullum karuwa yake a jihar tun bayan kammala zabubbukan shugaban kasa da gwamnoni har ma da na 'yan majalisun tarayya da na jihohi da suka gabata a kasar.

Kara karanta wannan

Hukumar NSCDC Ta Cafke Masu Kwacen Wayoyi 5 a Kano, Ta Farautar Masu Siyan Wayoyin

Jimami: Yan Bindiga Sun Kashe Aminin Bola Tinubu a Jihar Imo

A wani labarin, yan bindiga sun hallaka wani jigo a jam'iyyar APC a jihar mai suna Kyaftin Enock Tony, wanda ya kasance aminin zababben shugaban kasa Tinubu ne.

Legit.ng ta tattaro cewa tsagerun sun bindige Kyaftin din ne akan hanyarsa ta zuwa taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel