Hare-Haren Filato: Kungiyar CAN Ta Ba Wa Kiristoci Shawara Mai Muhimmanci

Hare-Haren Filato: Kungiyar CAN Ta Ba Wa Kiristoci Shawara Mai Muhimmanci

  • Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bukaci Kiristoci da su zauna lafiya da Musulmi don samun dorewar zaman lafiya
  • Kungiyar ta koka kan yadda sabbin hare-hare ke kara yawa musamman a kananan hukumomin Riyom da Mangu
  • A karshe kungiyar ta kirayi hukumomi da su dauki tsauraran matakai don ganin an kawo zaman lafiya a kasar baki daya

Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta koka kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ya yi kamari musamman a kananan hukumomin Mangu da Riyom na jihar Plateau, yayin da suka kirayi Kiristoci da kada su dauki doka da hannunusu.

Kungiyar ta ce akalla an kashe mutane fiye da 130 yayin da aka kona gidaje fiye da 1000 wanda ya shafi kauyuka 22.

Archbishop Daniel Okoh
Shugaban Kungiyar CAN Ta Najeriya Daniel Okoh. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar CAN ta Najeriya, Archbishop Daniel Okoh shi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Kotu ta Hana a Taba ‘Dan Majalisar Kano, Ado Doguwa Bisa Zargin Kashe Mutane

Ka da wanda ya dauki doka a hannunsa, CAN ta shawarci Kiristocin Plateau

Ta shawarci Kiristoci da kada wadannan hare-hare su harzuka su da zai kai ga daukar fansa wadda a karshe zai kara dagula al’amuran, cewar jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Cikin alhini muna jan hankalin ‘yan Najeriya akan sabbin hare-haren da suke kara faruwa a kananan hukumomin Mangu da Riyom da ke jihar Plateau a Najeriya.
“Hare-haren da ya fara afkuwa a kayukan Mangu a ranar Litinin 15 ga watan Mayu wanda ‘yan bindiga suka kai ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kauyukan da abin yafi shafa

Kauyukan sun hada da Fungzai da Hale da Kubwat da Bwoi da sauran kauyukan yankin Kombun da ke karamar hukumar Mangu.

Ya kara da cewa:

“Muna Allah wadai da wannan ta’asa ganin yadda mutane da dama ke hallaka da kuma rasa rayuka cikin mummunan yanayi.

Kara karanta wannan

Daliban Sheikh Abduljabbar Sun Zargi Malamai da Hada Kai Don Kawo Rudani a Shari’ar Malaminsu

“Muna godewa jami’an tsaro da kokarin da suke yi don ganin an samu zaman lafiya, muna kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su binciko masu laifin da kuma hukuntasu.
“A matsayina na shugaban addini, ina kira da mu rungumi zaman lafiya don kawo karshen bambace-bambancen da ke tsakaninmu, tashin hankali ba zai gyara komai ba sai dai kara tarwatsa zaman lafiya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“A karshe ina kira ga ‘yan Najeriya da ke kananan hukumomin Mangu da Riyom da kasa baki daya da su zauna lafiya, kada mu bari wani abu ya zo ya harzika mu don daukar fansa da ba zai kawo zaman lafiya ba sai dai ya kara lalata mana zaman lafiya.
“Ya kamata mu yi aiki tare wajen gina kasarmu inda kowa zai yi rayuwarsa cikin mutunci da tsaro, Allah ya taimaki Najeriya.”

Yadda Muka Rasa ’Yan Uwanmu a Harin ’Yan Bindiga a Jihar Plateau

Kara karanta wannan

Yadda Muka Rasa ’Yan Uwanmu a Harin ’Yan Bindiga, Mutane Sun Koka a Jihar Plateau

A wani labarin, wasu wadanda harin 'yan bindiga ya rutsa dasu sun koka kan yadda 'yan bindiga suka addabe su.

Hare-haren wadda ya shafi kananan hukumomin Mangu da Riyom ya afku ne a ranar Talata 16 ga watan Mayu wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel