'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Yan Bijilanti da Wasu Mutum 17 a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Yan Bijilanti da Wasu Mutum 17 a Zamfara

  • Yan bindigan jeji sun kashe akalla mutane 18 ciki harda shugaban 'yan sa'kai a kauyukan karamar hukumar Maru, jihar Zamfara
  • Wani ganau kuma ɗaya daga cikin jami'an 'yan sa'akai ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun yi musayar wuta
  • Mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya ce rahoto bai iso gare su ba zuwa yanzu

Zamfara - Aƙalla mutane 18 suka rasa rayukansu daga ciki harda shugaban jami'an yan banga a wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai ƙauyuka a jihar Zamfara.

Miyagun 'yan bindigan sun aikata wannan ɗanyen aiki ne a kauyukan da ke karkashin gundumar Ruwandoruwa, ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Harin yan bindiga.
'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Yan Bijilanti da Wasu Mutum 17 a Zamfara Hoto: channelstv
Asali: UGC

Wani ganau, Aminu Ilyasu, mamban tawagar yan bangan waɗanda aka fi sani da 'yan sa'kai ya tabbatar da faruwar lamarin ga Channels tv.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Umarci Jami'an DSS Da Su Bar Ofishin EFCC Cikin Gaggawa

A cewarsa, harin ya nuna dama 'yan fashin jejin sun nufi kashe shugaban 'yan sa'kai na ƙauyen Dangamji mai suna, Ɗahiru.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce maharan sun kashe shugaban yan banga, Ɗahiru Dangamji, tare da wasu mutane uku a wurin da suka ɓuya cikin daji a yankin ƙauyen Ɗanzara.

Iliyasu ya ce:

"Tun asali yan bindiga sun yi nufin farmakan shugaban yan sa'kai, Ɗahiru, suka kashe shi tare da wasu mutane uku a wurin da ya buya a yankin garin Danzara."
"Mun saba shiga cikin daji mu ɓoye saboda mun san yadda yan bindigan ke aikata ta'adinsu, haka su ma sun san muna shiga daji mu ɓoye musu."

Ya ƙara da cewa lokacin da labarin kashe Ɗahiru ya isa ƙauyen, nan take jami'an yan Sa'akai suka haɗu a Ruwandoruwa, suka durfafi yankin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗau Zafi, Ya Ce Zai Soke Lasisin Mallakar Duk Gidan Man da Ya Ɓoye Fetur Ko Ya Kara Farashi

Sai dai bisa rashin sa'a, 'yan bindigan suka musu kwantan ɓauna a kan Titin, suka buɗe musu wuta.

"Muna kan hanyar zuwa Ɗanzara muka ci karo da su a kan Titi, mun kwashe awanni muna musayar wuta, 11 daga cikinmu suka mutu yayin yan bindiga da dama suka sheƙa barzahu."
"Ina ganin idan zan iya tuno adadin daidai, mun kashe kusan mutum 10 daga cikinsu."

Har kawo yanzun hukumar yan sanda ba ta ce komai ba, muƙaddashin kakakin yan sanda a Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya ce ba su da masaniyar abinda ya auku.

Yan sanda sun kwace iko da zauren majalisa

A wani labarin kuma Dakarun 'yan sanda sun kewaye zauren majalisar dokokin jihar Filato da safiyar Laraban nan.

Mamban majalisar dokokin jihar, Honorabul Gwottson, mai wakiltar mazaɓar Jos ta kudu ne ya tabbatar da faruwar haka ga jaridar a Jos, babban birnin jihar Filato.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jim Kaɗan Bayan Rantsuwa, Gwamna Arewa Zai Ɗauki Matasa 20,000 Aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel