Sojoji Sun Ceto Mutum 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Zamfara, Sun Halaka 'Yan Bindiga Da Dama

Sojoji Sun Ceto Mutum 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Zamfara, Sun Halaka 'Yan Bindiga Da Dama

  • Dakarun sojoji sun samu nasarar ceto mutum 10 waɗanda aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara
  • Dakarun sojojin sun kuma samu nasara kan ƴan bindiga, inda suka tura da dama daga cikinsu inda idan aka je ba a dawowa
  • A lokacin fafatawar dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai da babura daga hannun miyagun ƴan bindigan

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin haɗin guiwa na atisayen Hadarin Daji a yankin Arewa masa Yamma, sun ceto wasu mutum 10 da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Dakarun sojojin a lokacin atisayen sun kuma halaka ƴan bindiga da dama a ƙaramar hukumar Anka ta jihar.

Channels Tv ta rahoto cewa dakarun sojojin sun ƙaddamar da farmakin ne a ranakun Talata, 30 ga watan Mayu da Laraba, 31 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mutane Sun Fara Zanga-Zanga Kan Tashin Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

Wani majiya mai tushe daga cikin jami'an tsaron wanda ya nemi da a sakaya sunansa, ya tabbatar da aukuwar hakan ga majiyarmu a ranar Alhamis.

Sojoji sun ceto mutanen da aka sace a Zamfara
Dakarun sojoji Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa dakarun sojojin sun gudanar atisayen ne da kakkaɓe ƴan bindiga a ƙauyukan Alasanawa, Kayawa, Mai-Zuma, Dutsi, Dogon Gandu, Girari, Maiwa, Asarara, Gabawuri, Tungan Danmada, Baje, Ruwaje, Atarawa, Zungo da Maniya duk a cikin ƙaramar hukumar Shinkafi.

Ƴan bindiga da dama sun halaka

A cewarsa, ƴan bindiga da dama sun baƙunci lahira a yayin bata kashin, sannan an kwato makamai da ƙona babura guda huɗu da ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su.

Haka kuma dakarun sojoji na Forward Operating Base (FOB) a ƙaramar hukumar Anka, sun kai farmaki a kan ƴan ta'adda a yankin.

Dakarun sojojin lokacin da su ke sintirin neman ƴan bindiga, sun ritsa su hanyar wucewarsu a ƙauyen Tungar Rakuma, inda suka yi musayar wuta da samun nasarar halaka ɗan bindiga ɗaya.

Kara karanta wannan

Bayan Rantsar da Sabon Gwamna, Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jami'an Tsaro da Wasu 17 a Jihar Arewa

A lokacin bata kashin dakarun sojojin sun kwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, babur guda ɗaya da harsasai da dama, yayin da da dama daga cikin ƴan bindigan suka arce da raunikan harbin bindiga.

Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Yan Bijilanti da Wasu Mutum 17 a Zamfara

A wani rahoton na daban kuma, ƴan binɗiga sun tafka mummunar ta'asa a ƙaramar hukumar Maru jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun kai hare-hare ne a ƙauyukan yankin inda suka halaka mutum 19 ciki har da shugaban ƴan bijilanti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel