'Yan Bindiga Sun Halaka Sufetan 'Yan Sanda Tare Da Raunata Wasu 'Yan Sanda Biyu a Jihar Ebonyi

'Yan Bindiga Sun Halaka Sufetan 'Yan Sanda Tare Da Raunata Wasu 'Yan Sanda Biyu a Jihar Ebonyi

  • Ƴan bindiga sun farmaki jami'an ƴan sanda suna tsaka da aikinsu cikin dare a jihar Ebonyi a yankin Kudu maso Gabas na Najeriya
  • Ƴan bindigan sun halaka sufetan ƴan ɗaya da raunata ƴan sanda biyu a farmakin da suka kai kan jami'an tsaron
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ana duba lafiyar jami'an ƴan sandan da suka samu raunika

Jihar Ebonyi - Ƴan bindiga sun bindige wani sufetan ƴan sanda har lahira, a birnin Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne ranar Lahadi da daddare, a shataletalen bankin Union wanda ya ke kusa da hedikwatar rundunar ƴan sandan jihar.

Yan bindiga sun halaka jami'in dan sanda a jihar Ebonyi
'Yan bindiga sun farmaki jami'an 'yan sanda a Ebonyi Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Ƴan bindigan sun buɗe wuta ne a wajen shingen binciken ƴan sandan, inda suka halaka sufetan nan ta ke.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Sanatan NNPP a Jihar Nasarawa, Ya Sha Da Kyar a Wani Mummunan Hari Da Aka Kai Masa

Haka kuma ƴan bindigan sun raunata wasu jami'an ƴan sanda mutum biyu, waɗanda suka samu raunika daban-daban, inda ake duba lafiyarsu a wani asibiti a cikin birnin Abakaliki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ƙara da cewa jami'an ƴan sanda biyu sun samu munanan raunika, sannan ana kula da lafiyarsu a wani asibiti.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Onome Onovwakpoyeya, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Talata da daddare.

Sanarwar na cewa:

"A ranar 22/05/2023 da misalin ƙarfe 8:30 na dare, jami'an rundunar mu waɗanda ke aikin binciken ababen hawa a shataletalen bankin Union, wanda ya haɗa bankuna da dama, sun yi musayar wuta da ƴan bindiga waɗanda ba a san abinda ya kawo su yankin ba."

Kara karanta wannan

Mutane Hudu Sun Faɗa Komar ‘Yan Sanda a Ogun Bisa Laifin Halaka Makiyayi

"Abin takaici, ɗaya daga cikin jami'an ya riga mu gidan gaskiya, yayin da wasu jami'ai biyu suka samu raunika inda ake basu kulawa a asibiti. Ƴan bindigan su ma sun yi asarar rayuka amma sun ɗauke gawargwakin."
"Domin haka kwamishinan ƴan sanda yana roƙon a kawo rahoton duk wanda ka gani da raunin harbin bindiga ko yana neman a yi masa magani."

'Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Halaka Dan Takarar Sanata a Nasarawa

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun kai farmaki kan ɗan takarar sanatan jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), a jihar Nasarawa.

Dr Waziri Kabir-Mohammed ya tsallake rijiya da baya a harin da ƴan bindigan suka kai masa har cikin gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel