Yan bindiga
Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga yayin wani artabun da suka yi a jihar Kano. Sojojin sun kuma kwata kayayyaki.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da jami'an tsaro da suka hada da sojoji, 'yan sanda, NSCDC da sauransu bayan harin 'yan bindiga a jihar Kano.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa yan bindiga sun fara addabar wasu yankunan jihar Kano da ake zargin suna kwararowa daga Katsina mai makwabtaka da su.
Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta yi karin haske kan sace mataimakin shugaban majalisar Kebbi, Alhaji Muhammad Sama’ila a Bagudo bayan sallah a masallaci.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kebbi. 'Yan bindigan sun yi garkuwa da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar.
Cocin HEKAN a Kaduna ya tabbatar da cewa an kashe Fasto Yahaya Kambasiya tare da sace mutane sama da 20 a wani sabon harin da ’yan bindiga suka kai a Jihar Kaduna.
Kungiyar JNIM da ake dangantawa da Al-Qaeda ta ce ita ta kai harin farko a Jihar Kwara da ke Arewacin Najeriya watanni bayan ayyana sababbin dakaru a kasar.
Wasu tsagerun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Sokoto. 'Yan bindigan sun kashe wani basarake tare da wasu mutane a yayin harin.
An kashe fitaccen kwamandan ’yan bindiga Jankare a rikici da abokan ta’addanci a yankin Dutsenma, jihar Katsina, bayan sabani kan sarauta da hare-hare.
Yan bindiga
Samu kari