Yan bindiga
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano, sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargin 'yan bindiga ne. An cafke su bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan miyagun 'yan bindiga a jihar Kebbi. Sojojin sun hallaka 'yan bindiga masu yawa bayan an gwabza fada.
'Yan bindiga sun saki mutum 19 da suka yi garkuwa da su a Katsina, bayan tattaunawar zaman lafiya karkashin shirin 'Operation Safe Corridor' a Katsina.
Sojan Najeriya ya rasa ransa bayan bin wani da ya kai musu hari da sanda a kauyen Twatagi, karamar hukumar Patigi, Jihar Kwara inda aka tsinci gawarsa.
Dakarun sojin Najeriya sun kai samame wurare da dama, inda suka yi nasarar kama jagoran dan ta'adda, Babawo Badoo. An kama wasu mutum 19 a yankin Bassa.
Wasu mutanen Kano da ke zaune a karamar hukumar Shanono sun koka kan hare haren 'yan bindiga da suke shigo musu daga Katsina. Sun nemi agajin Abba da Tinubu.
DSS ta kama masu safarar makamai uku a Kaduna, ta kwato AK-47 da alburusai sama da 200. Gwamna Uba Sani ya yaba, ya ce babu mafaka ga masu laifi.
A labarin nan, za a ji cewa dakarun hadin gwiwa a kasar nan sun yi nasarar kawar da yan ta'adda 50 tare da jikkata akalla 70 yayin hare-hare a Borno da Yobe.
Babban hafsan tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, ya bayyana cewa nan da wani lokaci kadan za a kawo karshen ayyukan 'yan bindiga da 'yan Lakurawa.
Yan bindiga
Samu kari