Yan Bindiga Sun Kai Sabon Farmaki, Sun Yi Awon Gaba da Babban Basarake

Yan Bindiga Sun Kai Sabon Farmaki, Sun Yi Awon Gaba da Babban Basarake

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙaramar hukumar Akpabuyo ta jihar Cross Rivers a daren ranar Lahadi
  • Miyagun ƴan bindigan a yayin farmakin da suka kai sun yi awon gaba da babban basaraken gargajiya na Akpabuyo
  • A yayin harin da ƴan bindigan suka kai sun kuma halaka wani hadimin basaraken wanda ya yi ƙoƙarin hana a ɗauke shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Cross Rivers - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da basaraken gargajiya na ƙaramar hukumar Akpabuyo ta jihar Cross Rivers, Etiyin Maurice Edet a gidansa.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan sun sace basaraken ne a daren ranar Lahadi, 10 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame fadar babban sarki, sun kwato makamai

Yan bindiga sun sace basarake a Cross Rivers
Yan bindiga sun yi awon gaba da basarake a Cross Rivers Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an harbe wani mai taimaka wa basaraken a yayin da aka yi garkuwa da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ta ce kawo yanzu ba ta samu cikakken bayani ba.

Sai dai wata majiya ta ce an kashe mai taimaka wa basaraken gargajiyar ne a lokacin da yake ƙoƙarin hana a sace shugaban nasa.

Garin Akpabuyo, wanda ya yi kaurin suna wajen aikata laifuka, bai wuce kilomita 15 ba daga Calabar, babban birnin jihar Cross Rivers.

Ƴan bindiga sun sako Farfesa

A halin da ake ciki kuma, masu garkuwa da mutane sun sako Farfesa Patrick Egaga na Jami’ar Calabar (UNICAL) bayan shafe kwanaki 26 a hannunsu.

An yi garkuwa da Egaga wanda shi ne Daraktan Servicom na jami'ar UNICAL a cikin rukunin gidajen ma’aikatan makarantar, inda waɗanda suka sace shi suka buƙaci a biya su kuɗin fansa naira miliyan 50.

Kara karanta wannan

An kuma: Yan bindiga sun kai sabon hari, sun yi garkuwa da ɗaliban jami'ar tarayya a arewa

An bayyana cewa an samu ƙaruwar aikace-aikacen masu garkuwa da mutane a Calabar da kewaye a watannin da suka gabata.

Mutanen da aka fi yin garkuwa da su yawanci sun haɗa da malaman jami'o'i, lauyoyi, likitoci, malamai da manyan mutane.

Ƴan Bindiga Sun Ƙona Gidan Basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kashe mutum hudu a kauyen Dungwel, karamar hukumar Mangu da ke jihar Plateau.

Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a ƙauyen sun kuma ƙona gidan basaraken ƙauyen wanda iyalansa ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel