'Yan Bindiga Sun Ƙara Kai Mummunan Hari Ƙauyuka 4 a Arewa, Sun Kashe Rayuka da Yawa

'Yan Bindiga Sun Ƙara Kai Mummunan Hari Ƙauyuka 4 a Arewa, Sun Kashe Rayuka da Yawa

  • Yan bindiga sun kai sabbin hare-hare wasu ƙauyaka a jihar Sakkwato sun kashe mutane akalla 9 ranar Litinin zuwa Talata
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kuma sace wasu da mutane da dama har da mata da kananan yara
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake jimamin kuskuren sakin bam kan masu bikin Maulidi a jihar Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu yayin da wasu gungun ƴan bindiga suka kai farmaki ƙauyuka huɗu a jihar Sakkwato daga ranar Litinin zuwa Talata.

Ganau sun shaida wa Premium Times cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mazauna kauyukan a hare-haren cikin kwanaki biyu kaɗai.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin masu maulidi yan bindiga sun halaka mutum 33 a wani sabon hari

Yan bindiga sun sake kai hari Sokoto.
Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kari Kauyuka Huɗu a Sokoto, Sun Hala Rayuka 9 Hoto: Premiumtimes
Asali: Twitter

A cewar mazauna yankin, ƴan bindigan sun kai farmaki kauyen Kajiyo a karamr hukumar Goronyo, Chaco a ƙaramar hukumar Wurno, Lambar Rabah a ƙaramar hukumar Rabah ranar Litinin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Washe gari kuma maharan suka sake shiga kauyen Rara da ke ƙaramar hukumar Rabah ranar Talata duk a jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yamma.

Yadda yan ta'adda suka tafka ɓarna a kuyukan

Mazauna sun ce yan bindigan sun kashe mutum huɗu tare da sace wasu 13 a kauyen Kajiyo yayin da suka yi ajalin rayuka uku a kauyen Lambar Rabah.

Haka nan kuma sun halaka mutum biyu kana suka yi awon gaba da wasu da dama a kauyen Rara, yayin da suka yi garkuwa da jama'a masu yawa a Chaco.

Wani mazaunin garin Rara mai suna Abubakar, ya ce:

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Sanata ya faɗi matakin da zasu ɗauka domin tabbatar da adalci kan kisan masu Maulidi

"Sun sace matana guda biyu, lokacin da suka shigo garin da daddare ranar Talata, mafi akasarin mutane sun ruga cikin gida, a tunanin su yan ta'addan kayan abinci kaɗai zasu ɗauka."
"Da yawa sun ɗauka zasu sace duk wanda suka haɗu da shi ne kawai amma sai suka shiga gida-gida, garin haka ne suka ɗauki matana guda biyu."

Mutumin ya bayyana cewa ba ya gida lokacin da yan bindiga suka suka shiga kauyen har suka ɗauki matansa, rahoton Sahara Reporters.

Wani mazauni na daban, Ibrahim Halilu ya ce dan uwansa Hussaini Bello na cikin wadanda aka yi garkuwa da su a harin wanda ya dauki tsawon sa’o’i.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i, bai amsa kira da sakon da aka aika masa kan sabbin hare-haren ba.

Yan bindiga sun farmaki jami'an NDLEA

A wani rahoton na daban kun ji cewa An yi wa jami’an NDLEA kwanton ɓauna a dajin Opuje da ke ƙaramar hukumar Owan ta Yamma a jihar Edo

A cewar hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a safiyar ranar Alhamis, jami’ai uku sun jikkata yayin harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel