Yan Bindiga Sun Tarwatsa Mutanen Gari Guda, Sun Tafka Mummunar Ɓarna Tare da Kashe Bayin Allah

Yan Bindiga Sun Tarwatsa Mutanen Gari Guda, Sun Tafka Mummunar Ɓarna Tare da Kashe Bayin Allah

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai mummunan harin kauyen Kidandan da ke yankin ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna
  • Mazauna garin maza da mata da ƙananan yara sun tattara sun bar garin bayan harin wanda yan bindigan suka kashe mutane da yawa
  • Wani mutumi ya ce maharan sun matsa wa garin ne bayan manoma sun kasa biyan harajin da suka ƙaƙaba musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Ɗaruruwan mutane sun tattara ƴan kayyakinsu sun bar gidajen su a ƙauyen Kidandan da ke ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Hakan ya biyo bayan mummunan farmakin da ƴan bindiga suka kai ƙauyen, suka shafe tsawon sa'o'i suna harbi kan mai uwa da wabi, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Yan bindiga sun tarwatsa gari guda a jihar Kaduna.
Yan Bindiga Sun Tarwatsa Garin Kidandan a jihar Kaduna, sun tafka barna Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Yayin harin, ƴan bindigan sun halaka bayin Allah da dama, kuma sun yi garkuwa da wasu domin neman kuɗin fansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna garin da suka tsira daga harin sun shaida wa yan jarida cewa 'yan bindigan sun tarwatsa garin ne saboda wasu manoma sun gaza biyan kuɗin haraji.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya bayanansa ya ce:

"Tsawon kwanaki 6 yan bindiga suna shigowa Kidandan suna cin karensu babu babbaka, amma wannan harin ya fi kowanne muni. Sun shigo sun ci mana mutunci sun tafi da mutane."
"Duk wanda ka gani a Kidandan yana rayuwa ne cikin tsoro, kullum matan mu da ƙananan yara guduwa suke su bar gari. Suna komawa wuri mai tsaro kamar Zariya."

Jami'an tsaro ba su zama a garin Kidandan

Ya ce maimakon a turo jami'an tsaro su zauna koda yaushe a garin, suna zuwa ne kawai su yi sintiri su tafi wanda hakan ya ba yan bindiga damar shigowa lokacin da babu jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin farmaki kan tawagar ƴan kwallon jihar APC, sun yi musu mummunar illa

Wannan hari na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan jirgin sojojin ƙasan Najeriya ya jefa bam kan masu bikin Maulidi a kauyen Tudun Bari, ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna, rahoton Daily Trust.

Wani mazaunin yankin Giwa, Aliyu Taheer, ya tabbatar wa Legit Hausa mafi akasarin mutanen Kidandan sun yi gudun hijira saboda ta'addancin yan bindiga.

A cewarsa, ko a ranar Jumu'a da ta gabata yan bindiga sun shiga garin sun kashe mutane ba tare da wata matsala ba domin jami'an tsaro ba su kai ɗauki ba.

Mutumin ya ce:

"Ko a jiya (Jumu'a) sun shiga garin sun kashe mutane uku, a yanzu sauran mutane sun gudu sun bar Kidandan domin tsira daga harin yan bindiga."
"Muna kira ga gwamnatin Kaduna ta ƙara miƙewa tsaye kan waɗannan mutanen domin kullum abun ƙara ƙaruwa yake, a baya mun fara ganin sauaƙi amma yanzu yana neman dawowa."

Ribadu da Sanatocin Arewa Sun Ziyarci Tudun Biri

Kara karanta wannan

An kuma: Yan bindiga sun kai sabon hari, sun yi garkuwa da ɗaliban jami'ar tarayya a arewa

A wani rahoton na daban Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ya ziyarci kauyen Tudun Biri don yin jaje ga al'ummar yankin.

Haka kuma, sanatocin arewa ma sun kai ziyara yankin da sojoji suka sakarwa masu Maulidi bama-bamai bisa kuskure wanda ya yi sanadiyar rasa rayuwa da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel