Yan bindiga
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa zai cigaba da ragargazar 'yan ta'adda a fadin Najeriya. Shugaban kasar ya bukaci hadin kan 'yan kasa.
Jihohin Kudu maso Yamma na tunkarar barazanar tsaro daga ‘yan bindiga da mayakan ISWAP yayin da DSS ta kama mutum 10 da ake zargi da ta’addanci a shiyyar.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya bukaci a karawa ma'aikatar tsaro karin kudade domin magance matsalolin rashin tsaron da ake fama da su a kasar nan.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro a jihar Zamfara sun samu nasara kan 'yan bindiga. Sojojin sun aika da wasu tsageru masu tayar da kayar baya.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki kan matafiya a jihar Kogi. Ƴan bindigan sun sace fasinjoji masu yawa ciki har da wasu jami'an sojoji.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jama'ar kasar nan su sa rai da samun faduwar turakun wutar lantarki saboda wasu dalilai da har yanzu ba a magance ba.
Dakarun tsaro sun kashe Idi Mai Randa da Ya’u a Zamfara. An samu nasara mai girma a yaki da 'yan fashi tare da kakkabe maboyarsu a jihohin Arewa maso Yamma.
Gwamna Zulum ya yi Allah-wadai da kisan manoma 40 a Dumba, ya ja kunnen jama'a su zauna cikin yankunan tsaro don kare rayuwarsu daga barazanar 'yan ta'adda.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ba da shawara ga jihohin Arewacin Najeriya masu fama da matsalar rashin tsaro. Ya bukaci su yi koyi da tsarin da ya kawo.
Yan bindiga
Samu kari