Yan bindiga
Wasu bama-bamai da aka binne a hanyar Borno zuwa Adamawa ta yi sanadin mutuwar mutum 2, bayan motarsu da ke kan hanyar kasuwa ta taka IED a hanyar zuwa kasuwa.
Dakarun Operation Fansan Yamma sun kashe Kachalla Na Faranshi a dajin Zurmi. Na Faranshi ya shahara wajen safarar makamai da kai hare-hare a Arewa maso Yamma.
'Yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Sabuwa da ke Katsina, inda suka kashe mutane biyu, suka sace wasu, amma 'yan sanda sun ceci mutane 13 yayin dakile harin.
Bayan zargin shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani kan girke Lakurawa domin kawo cikas a mulkinsa, Majalisar Dattawa za ta yi bincike domin gano gaskiya.
Rundunar 'yan sanda a jihar Akwa Ibom ta kama wani dan firamare mai shekaru 13 da ya ce makaranta da bindiga yana barazanar harbin dalibai. An kama mahaifinsa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Bola Tinubu ya magance matsalar tsaro ne babban abin da ya saka a gaba. Ya ce zai tallafawa sojoji a Najeriya domin yakar 'yan ta'adda.
Ministan tsaron Najeriya muhammad Badaru Abubakar ya ce cikin shekara daya za a shawo matsalar tsaro. Ya ce Tinubu ya hura musu wuta kan tsaron Najeriya.
Rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta kai farmaki maboyar 'yan ta'adda a Alkaleri inda ta yi jina jina ga 'yan ta'addar da kashe wasu biyu da kwato makamai.
An kashe jami’an tsaro 326 a Najeriya cikin shekara guda. Ƴan sanda 258, sojoji 59 sun mutu yayin da su ma NSCDC da hukumar shige da fice suka rasa jami’ansu.
Yan bindiga
Samu kari