'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Sarki Mai Martaba A Jihar Filato

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Sarki Mai Martaba A Jihar Filato

  • "Yan bindiga sun bi dare, sun yi awon gaba da Sarki a Masarautar Tal, Karamar hukumar Pankshin, jihar Filato ranar Litinin
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun shiga yankin da misalin ƙarfe 1:00 na daren wayewar garin yau, suka sace Alhaji Dabo Gutus
  • Ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Pankshin ya bukaci mutane su kwantar da hankulansu kuma su cigaba da harkokinsu

Plateau - Wasu tsagerun 'Yan bindiga a farkon awannin Litinin (yau) sun yi awon gaba da Sarkin gargajiya na masarautar Tal da ke ƙaramar hukumar Pankshin a jihar Filato, Alhaji Dabo Gutus.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa basaraken da ya shiga hannun 'yan ta'adda shi ke rike da Sarautar da ake kira, "Ngolong Tal" (Sarki mai daraja ta uku). An ce sun sace shi da misalin ƙarfe 1:00 na dare.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Ɗan Takarar NNPP Wuta a Jihar Arewa

Yan bindiga sun kai hari Filato.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Sarki Mai Martaba A Jihar Filato Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Wani mazaunin yankin Masarautar yace mutane na ƙoƙarin tuntuɓar masu garkuwa da mutanen domin jin menene asalin matsalar da ta kai ga sace sarkinsu.

Mamba mai wakiltar mazaɓar Panshin ta kudu a majalisar dokoki, Prince Dakup Ezra, ya yi kira ga al'umma su kwantar da hankulansu kan lamarin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ɗana majalisar ya ƙara da cewa a halin yanzun dawowar Basaraken cikin ƙoshin lafiya shi ne abu mafi muhimmanci da suka sa a gaba, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Ya kuma bukaci ɗaukacin mutanen mazaɓarsa da yankin masarautar su cigaba da harkokinsu na yau da kullum, kana su guji duk wani abu da ya shafi ɗaukar doka a hannu.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Yayin da aka tuntuɓi kakakin hukumar 'yan sanda ta jihar Filato, Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin na garkuwa da Basaraken. Ya ƙara da cewa tuni jami'ai suka bazama don gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

"Ba Kuskure Bane" Jam'iyyar APC Ta Faɗi Dalilin Sanya Jigon PDP a Kamfen Tinubu, Ta Maida Martani Ga Gwamnoni

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Halaka Babban Ɗan Sanda, Sun Yi Garkuwa da Matafiya a Jihar Buhari

Wasu tsagerun 'yan bindiga sun harbe Insufektan 'yan sanda har lahira a kan titin Katsina zuwa Jibiya.

Rahoto ya nuna cewa mamacin ya yi kokarin daƙile harin yan ta'addan ne amma ya gamu da ajalinsa, sun yi awon gaba da matafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel