Gwamnan Arewa Ya Ayyana Hukuncin Kisa Kan Yan Bindiga, Ya Bayyana Dalili

Gwamnan Arewa Ya Ayyana Hukuncin Kisa Kan Yan Bindiga, Ya Bayyana Dalili

  • Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya tabbatar da hukuncin kisa kan yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauransu
  • Matawalle ya ce ya yi amfani da manufofi da dama don magance matsalar rashin tsaro a jihar amma abun bai cimma nasara dari bisa dari ba
  • Gwamnan ya bayyana yan bindiga da masu garkuwa da mutane a matsayin dabbobi wadanda suka cancanci mutuwa

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya kafa hujja kan hukuncin kisa da aka amince dashi kan duk wanda aka kama da laifin fashi da makami, garkuwa da mutane, satar dabbobi ko ta’addanci a jihar.

Matawalle wanda yayi magana a ranar Laraba, lokacin da aka yi masa tambayoyi a wani shiri na gidan talbijin din TVC.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Mayarwa Buhari Martani Bayan Ya Tsawatar Masa Kan Siyawa Jami'an Tsaron Jiharsa Makamai

Bello Matawalle
Gwamnan Arewa Ya Ayyana Hukuncin Kisa Kan Yan Bindiga, Ya Bayyana Dalili Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewarsa, gwamnatin jihar ta gwada dabaru da dama don kawo karshen ta’addanci a jihar, amma wadannan matakan basu cimma nasara dari bisa dari ba.

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Allah ya sani nayi amfani da mafita da dama don wannan rikicin ya bar jihar, amma abun bakin ciki, akwai mutanen kirki da bara gurbi a kowace al’umma.
“Mun yi iya abun da za mu iya. Na yi amfani da dabaru da dama a jihar kuma yawancin dabarun sun haifar da sakamako iri-iri.
“Na yi sulhu. Na dauke sabis. Mun yanke hanyar tura abinci kuma mun ga nasarori, amma ba dari bida Dari ba. Yan bindiga na tsoton Yansakai saboda suna amfani da makaman da aka kirkira. Suna saka filog din babur a ciki. Yan bindiga na tsoron wannan makamin; makamin na raba yan bindiga gida biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 4 na Najeriya da Nijar Sun yi Muhimmiyar Ganawa a Maradi

“Suna kallon Yansakai a matsayin mugayen mutane. Na san dalilin da yasa na bayar da umurnin kuma nayi nasara kan wannan umurni da na bayar.”

Da aka tambaye shi kan ko hukuncin kisan zai yi aiki a jihar duba ga cewa ba abune da ya samu karbuwa ba a duniya, gwamnan yace yana da tabbacin zai yi aiki, rahoton The Cable.

“Hukuncin kisan zai yi aiki. Na rattaba hannu a kai. Duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci doka.Ba lallai ne hukuncin ya samu farin jini ba, amma wadanda ke kashe mutane, suna da farin jini?"

Da yake jawabi kan umurnin cewa mazauna su kare kansu da makamai, gwamnan yace yan bindiga basu cancanci yafiya ba.

'Yan Banga Sun Tarfa 'Yan Bindiga A Wata Jahar Arewa, Sun Hallaka 31

A wani labarin, kungiyoyin yan banga sun kashe ‘yan bindiga 31 a garin Kanoma da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta tasa keyar wani sarkin gargajiya zuwa gidan yari saboda laifuka biyu

Ku tuna cewa a ranar Lahadi da ya gabata, yan bindiga sun farmaki garin inda suka kashe mutane uku da kuma sace masu jego takwas.

Wani haifaffen garin, Abubakar Ibrahim, ya sanar da jaridar Punch cewa maharan da suka farmaki garin a ranar Lahadi da ya gabata sun yi shirin kai sabon hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel