‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Mai Ciki, Sun Bukaci N50m Ko Su Hallaka ‘Dan Jinjiri

‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Mai Ciki, Sun Bukaci N50m Ko Su Hallaka ‘Dan Jinjiri

  • ‘Yan bindiga sun dauke wasu mata ‘yan gida daya da suke zaune a Unguwar Mando tun a watan Yuli
  • ‘Yanuwan wadannan mutane sun ce ana neman N50m a matsayin fansar matan da jaririn da aka haifa
  • A cikin matan da aka yi awon-gaba da su akwai mai dauke da juna biyu, a wannan yanayi ne ta haihu

Kaduna – Miyagun ‘yan ta’adda sun sace wasu ‘yan mata uku daga gida daya, daga cikunsu har da wanda take dauke da juna biyu a garin Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto a yammacin Litinin, 26 ga watan Satumba 2022 cewa ‘yan bindigan suna barazanar kashe wadannan Bayin Allah.

‘Yan ta’addan sun bukaci a biya Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansar mutanen da ke tsare. Daga ciki har da jaririn da Zainab ta haifa a hannunsu.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Sheke Manoma 3, Sun yi Garkuwa da Wasu 22

Punch tace ana haka ne wata matar aure daga cikin matan mai suna Zainab ta haihu a jeji.

N6.5m tayi kadan

Dangi sun roki gwamnati ta taimaka masu wajen kubutar da ‘yanuwan na su, suka ce sun iya tara N6.5m, amma ‘yan bindigan sun raina wannan kudi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kabir Yusuf ‘danuwa ne ga matan, kuma shi ne yake faman tattaunawa da ‘yan bindigan domin ganin an iya cin ma matsaya wajen biyan kudin fansar.

‘Yan Bindiga
Mafakar 'Yan biniga, Dajin Kamuku Hoto: @defensenigeria
Asali: Twitter

Malam Yusuf ya fadawa manema labarai da farko an nemi N140m a hannunsu. Sannu a hankali aka yi ta rage kudin, har aka tsaya yanzu a kan N50m.

Dole sai an biya N50m - 'Yanuwa

“Tun da suka yi garkuwa da su muke tattaunawa da su. ‘Yan ta’addan sun bukaci N140m da farko, amma muka roke su, muka fada masu mu talakawa ne.

Kara karanta wannan

Da Gaske Aure Za Su Yi? Hotunan Hauwa Ayawa da Umar Gombe Ya Haddasa Cece-kuce A Soshiyal midiya

Sai suka rage shi zuwa N100m. Muka sake rokonsu, daga baya suka mai da shi N50m. Sun yi barazanar idan ba mu da N50m, ka da mu sake kiransu a waya.
Abin takaicin shi ne a ranar Lahadi nayi magana da masu garkuwa, na roki su saki ‘yanuwana da jaririn da aka haifa, N6.5m kurum muka samu.
Daga nan sai suka yi ta zagi na. Suka fada mani idan bamu kawo N50m nan da kwanaki biyu ba, za su kashe duka ‘yanuwa na da ‘dan jaririn.

- Kabir Yusuf

'Yanuwa suna cikin zullumi

Fiye da watanni biyu da suka wuce, ‘yan ta’adda suka je gidan wadannan mutane da ke unguwar Mando a karamar hukumar Igabi, suka yi awon gaba da su.

Ku na da labari har zuwa yanzu jami’an tsaro ba suyi nasarar ceto ‘yan gida dayan ba. Ita dai Gwamnatin Kaduna ba ta goyon bayan kudin fansa ga miyagu.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka

Asali: Legit.ng

Online view pixel