'Yan Banga Sun Tarfa 'Yan Bindiga A Wata Jahar Arewa, Sun Hallaka 31

'Yan Banga Sun Tarfa 'Yan Bindiga A Wata Jahar Arewa, Sun Hallaka 31

  • Tsagerun yan bindiga sun hadu da ajalinsu yayin da suka yi kokarin sake kai farmaki garin Kanoma da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara
  • Yan banga a garin Kanoma da kauyukan da ke kewaye sun hada hannu inda suka farmaki mayakan a jeji
  • Yan ta'adda 31 ne suka hallaka yayin da wasu da dama suka tsere da manyan raunuka

Zamfara - Kungiyoyin yan banga sun kashe ‘yan bindiga 31 a garin Kanoma da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Talata.

Ku tuna cewa a ranar Lahadi da ya gabata, yan bindiga sun farmaki garin inda suka kashe mutane uku da kuma sace masu jego takwas.

Zamfara
'Yan Banga Sun Tarfa 'Yan Bindiga A Wata Jahar Arewa, Sun Hallaka 31 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wani haifaffen garin, Abubakar Ibrahim, ya sanar da jaridar Punch cewa maharan da suka farmaki garin a ranar Lahadi da ya gabata sun yi shirin kai sabon hari.

Kara karanta wannan

An gano wata maboyar 'yan bindiga a Arewa, an fatattaki tsageru, an ceto mutanen da aka sace

Ibrahim ya ce yan bangan garin Kanoma da wadanda ke kauyukan da ke kewaye sun yi gaba da gaba dasu bayan sun samu labarin cewa yan bindigar na shirin sake kai hari garin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ibrahim ya ce:

“Kungiyoyin yan bangar sun samu labari cewa yan bindigar, wadanda suka kasance kan babura suna a hanyarsu ta zuwa garin Kanoma don kaddamar da wani harin.
“Saboda haka yan bangar na samun labarin, sai suka tara kansu sannan suka gayyaci sauran kungiyoyin yan banga da ke kauyukan kewaye wadanda suka zo suka taimaka.”

Ibrahim ya ce an sanar da jami’an sojin da aka zuba a garin game da lamarin amma babu wanda ya zo a cikinsu.

Ibrahim ya bayyana cewa kungiyoyin yan bangan sun tafi jeji daga inda yan bindigar suke fitowa sannan suka kai kwantan bauna.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Ya ce:

“Yan bindigar na matsowa kusa da inda kungiyoyin yan bangar suke boye sai aka far masu sannan suka fara gudun neman tsira saboda basu yi tsammanin kowani hari ba.
“Kungiyoyin yan bangar sun yi nasarar kashe yan bindiga 31 nan take; domin an kirga gawarwakinsu, yayin da sauran suka tsere da raunin harbi masu muni.”

Ibrahim ya kara da cewar yan bindigar sun koma wajen sannan suka kwashe wasu daga cikin gawarwakin inda suka kona sauran.

Punch ta kuma rahoto cewa ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ba don baya daga wayarsa kuma bai amsa sakon da aka aike masa ba.

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

A wani labarin, mun ji cewa tsagerun yan bindiga sun kashe jami’an sojoji guda biyar da wani dan farin hula daya.

An tattaro cewa lamarin ya afku ne a kusa da wani banki a Umunze, yankin karamar hukumar Orumba ta kudu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda Da Wasu 3, Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Masu Yawan Gaske A Jihohin Arewa 2

Wata majiya da ta zanta da jaridar ta bayyana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 2:00pm na ranar Laraba, 28 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel