Yan Ta'adda Sun Sake Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kashe Masallata Da Yawa

Yan Ta'adda Sun Sake Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kashe Masallata Da Yawa

  • Yan bindiga sun kai hari a masallacin Juma'a na garin Ruwan Jema a karamar hukumar Bukkuyum na Jihar Zamfara
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun bindige masallata guda 15 har lahira sannan sun raunata wasu da dama
  • Yan bindigan sun taho masallacin ne kan babura kamar za su yi sallah amma ana fara sallar sai suka bude wa mutane wuta

Jihar Zamfara - Yan bindiga sun kai hari masallacin Juma'a da ke garin Ruwan Jema a karamar hukumar Bukkuyum na Jihar Zamfara suka kashe mutane 15, Nigerian Tribune ta rahoto.

Harin na baya-bayan nan ya faru ne makonni uku bayan yan ta'adda a ranar Juma'a sun kai hari a masallaci a garin Zugu a karamar hukumar inda suka kashe mutum 45.

Taswirar Jihar Zamfara.
Zamfara: Yan Bindiga Sun Bude Wa Masallata Wuta A Masallacin Juma'a, Sun Bindige 15 Har Lahira. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Budewa Motocin Tawagar Kamfen Sanata Uba Sani Wuta A Kaduna, An Sace Jiga-Jigan APC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani mazaunin garin, Ahmed Bukkuyum ya ce yan bindigan sun boye Ak 47 dinsu cikin tufafinsu suka yi kamar sun taho yin sallah ne.

Ya ce:

"Sun taho masallaci kan babura amma babu wanda ya zargi cewa yan bindiga ne. Mun yi tunanin cewa sun zo sallar Juma'a ne."

An tattaro cewa bayan an fara sallar, bata garin suka bude wa masallata wuta.

A yayin hakan, an ce, sun bindige masallata 15 har lahira, yayin da wasu masallata da dama suka jikkata.

A cewar majiyar, akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ya karu domin akwai mutane da dama da ba a gano su ba.

A lokacin hada wannan rahoton, babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar ko yan sanda.

An Kama Ƴan Ta'addan Da Suka Sace Mahaifiyar Sanatan APC a Kano Da Kuma Kashe Jami'an Tsaro

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da bam ya tashi bayan sallar Juma'a, mutane da dama sun mutu

A wani rahoton, yan sanda a Jihar Jigawa sun kama mutane biyu da ake zargi da kashe jami'in hukumar shige da fice da kuma garkuwa da mahaifiyar sanatan APC mai wakiltar Kano ta tsakiya, Abdulkarim Abdulsalam.

Kakakin yan sandan jihar, Lawal Adam, ya ce yan sanda da yan bijilante ne suka gano wadanda ake zargin a wurare daban-daban a Kano da Jigawa, rahoton Premium Times.

A watan da ta gabata, Premium Times ta rahoto yadda yan ta'adda suka kashe jami'in shige da fice ɗaya suka raunata wasu biyu a karamar hukumar Birniwa, da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel