Sojoji Sun Hallaka Jagororin ‘Yan Bindiga da Wasu Miyagu Barkatai a Katsina da Zamfara

Sojoji Sun Hallaka Jagororin ‘Yan Bindiga da Wasu Miyagu Barkatai a Katsina da Zamfara

  • Sojojin Najeriya sun shiga inda ‘yan bindiga suke, sun yi masu raga-raga a yankunan Katsina da Zamfara
  • A irin wadannan hare-hare ne ake zargin an bindige Dogo Rabe, wanda Kauyukan Zamfara sun san da zaman shi
  • Luguden sojoji ya dura gidan Gwaska Dankarami, amma babu tabbacin an yi nasarar kashe wannan ‘dan bindiga

Zamfara - Hatsabibin ‘dan bindigan nan, Dogo Rabe yana cikin wadanda ake tunanin an kashe a wani hari da sojojin sama suka kai a makon jiya.

Premium Times ta kawo rahoto a ranar Juma’a cewa an kashe Dogo Rabe da wasu miyagun ‘yan bindiga 45 da suka addabi yankunan jihar Zamfara.

Luguden wutan da sojojin saman suka kai yana cikin kokarin da ake yi da jirgi wajen ganin bayan ‘ta’addan da ke tsakanin Zurmi da Birnin Magaji.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Fara Tonuwa da Sojoji Suka yi Ram da Masu Taimakon 'Yan Garkuwa da Mutane

Wata majiya tace sojoji sun rutsa ‘yan ta’addan da ke yankunan Jibia a Arewacin Katsina.

Wani ‘dan jaridar BBC Hausa mai suna Abdulbaqi Aliyu Jari, ya shaida ‘yan ta’adda akalla 40 suka mutu a harin da sojoji suka kai Birnin Magaji.

Sojoji sun shiga Zurmi

A garin Zurmi, wani mazauni mai suna Abdullahi Mamman ya shaida cewa ‘yan ta’ada sun gamu da iyakarsu a harin da aka kai masu a Lambar Gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Super Tucano
Jirgin A29 Super Tucano Hoto: Humanglemedia.com
Asali: UGC

A wannan gari na Lambar Gabas, akwai wani shahararren ‘dan bindiga da ake kira Gwaska Dankarami.

Daily Post tace babu wanda zai iya cewa ga adadin miyagun da suka mutu, amma dai an budawa gidan Dankarami wuta, amma ba a same shi ba.

Dogo Rabe ya mutu a Katsina?

Haka zalika mutanen Jibia sun shaida cewa an kashe Rabe a wajen wadannan hare-hare. Ana tunanin abin ya faru ne a hanyarsa ta zuwa Zurmi a Zamfara.

Kara karanta wannan

‘Yan damfara Sun yi wa Asusun Bayin Allah Tas a Banki, Sun Sace Naira Miliyan 523

Wani mazauanin wannan gari da ke kan iyaka da kasar Nijar, yace mutane biyar ake tunani suna tare da Rabe a lokacin da dakarun sojoji suka rutsa su a jeji.

Sojojin sama sun tabbatar da cewa dakarun Katsina 213 Forward Operation Base sun yi amfani a jirage, sun kai wa miyagun ‘yan bindiga hari a Zurmi da Jibia.

Bello Turji ya kubuta

Mun fahimci labarin hallaka Dogo Rabe ya zo ne bayan ‘yan kwanaki da aka ji jiragen yaki sun rutsa Bello Turji a wajen wani biki, har aka kusa hallaka shi.

An ji cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun samu labarin ‘yan bindiga za su taru a garinsu Bello Turji domin bikin suna, sai aka kai masu hari nan-take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel