Jihar Ekiti
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhihinsa kan kisan da aka yi wa wasu sarakunan gargajiya a Ekiti, ya kuma umarci ceto daliban da aka sace a jihar.
Wani dan majalisar wakilai ya kasa danne zuciyarsa kan matsalar tsaron da ake fama da ita a jihar Ekiti. Dan majalisar ya fashe da kuka yayin da ya nemi a kai dauki.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da wasu yara ‘yan makaranta da ba a tantance adadinsu ba a karamar hukumar Emure da ke jihar Ekiti.
An shiga tashin hankali bayan 'yan bindiga sun yi ajalin wasu manyan sarakunan gargajiya a karamar hukumar Ikole da ke jihar Ekiti a Kudancin Najeriya.
Masu garkuwa da mutane sun sace wasu mutane da ba a san adadinsu ba a hanyar titin Akure/Ikere. Jami'ar Yan sanda Funmi Odunlami ta tabbatar da lamarin.
A wani abu kamar almara, wasu 'yan daba sun farmaki asibitin Ekiti kuma sun yi awon gaba da wata gawa. Lamarin ya faru a ranar Litinin, inda suka lalata kayayyaki.
Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti ya shaida rantsuwar kama aikin sabbin ciyamomi 38 da mataimakansu, ya ja kunnensu kan sha'anin tsaro a yankunan su.
Kayode Fayemi ya sa ran zama ministan harkokin kasar waje ne, amma sai ga shi ba hakan ta faru ba, ya ce kiris ya rage ya ajiyewa Muhammadu Buhari kujerarsa.
Cif Sanya Atofarati ya kafa tarihi a kundin bajinta na Guinness bayan shafe awanni 120 ya na kallon talabijin a jihar Ekiti a yau wanda ya fara tun ranar Laraba.
Jihar Ekiti
Samu kari