Jihar Edo
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ce nasarar APC a zaben Edo ya nuna akwai alamar talakawa sun amince da salon mulkin Bola Tinubu.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murna bayan APC ta lashe zaben gwamna a jihar Edo. Buhari ya bukaci yan takaran PDP da APC su hada kai domin cigaba a Edo.
Dan takarar jam'iyyar APC, Monday Okpebholo ya samu nasarar cin zabe a kananan hukumomi 11 cikin 18 a zaben jihar Edo da aka gudanar tare da samun kuri'u 291,667.
A ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba ne hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben jihar Edo daga kananan hukumomi 18. Jam'iyyar PDP ta lashe zabe a 7 cikin 18.
Bayan shafe awanni ana tattara sakamakon zaben jihar Edo, Hukumar zabe ta INEC bayyana Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.
Yayin da ake dakon sakamakon zaben jihar Edo, Gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya sun tura sako ga hukumar zabe ta INEC game da yin adalci a zaben.
Jam'iyyar PDP ta bayyana rashin gamsuwa da alkaluman da su ka fito daga kananan hukumomin Egor da Akoko Edo bayan hukumar INEC ta fadi sakamakon su.
Dan takarar APC a zaben gwamnan jihar Edo da aka yi ranar Asabar, Sanata Monday Okpebholo, ya fara hangen nasara a zaben bayan APC ta ba PDP tazarar kuri'u 54,437.
Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar APC ita ce a kan gaba bayan da hukumar zabe ta INEC ta bayyana sakamakon kananan hukumomi 13 na jihar Edo a ranar Lahadi.
Jihar Edo
Samu kari