Hukumar DSS
Jami'an tsaro na hukumar DSS da sojoji sun yi gumurzu da 'yan bindiga a jihar Neja. Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga da dama yayin artabun.
Sarkin Musulmi a Najeriya, Sultan Sa'ad Muhammad Abubakar ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda yake karfafa zaman lafiya tsakanin addinai.
A wannan labarin, za ku ji DSS ta cafke mutum 4 da ake zargi da ta’addanci da garkuwa da mutane a Sakkwato da Abuja yayin tantance maniyyata Hajji.
Dakarun hukumar tsaron farin kaya sun kara samun nasarar damke wani jagoran dabar masu garkuwa da mutane a lokacin da yake shirin tafiya sauke farali a Saudiyya.
DSS ta kama Sani Galadi a Sokoto yana kokarin tafiya aikin Hajji. Ana zargin Galadi da garkuwa da mutane a Zamfara, kuma yanzu haka yana hannun DSS domin bincike.
Jami'an DSS sun kama Yahaya Zango, hatsabibin mai garkuwa da mutane a sansanin alhazai na Abuja. Jama’a na tambaya: me zai faɗa wa Allah kan ta'addancinsa?
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa DSS kan kama masu garkuwar da suka sace yarinya mai shekara 1 suka wurga ta rijiya bayan karbar kudin fansa.
Kasar Birtaniya ta yi magana kan tsohon sojanta da aka kama da Bindigogi a Najeriya. An kama mutumin da bindigogi kirar AK47 fiye da 50 a jihar Delta.
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa DSS sun kama wani jami'i tsaro bisa zargin sayar da makamai ga 'yan bindiga. An kama wasu tarin 'yan bindiga 53.
Hukumar DSS
Samu kari