Jami’an Tsaro Sun Kama Mahdi da Ya Roki Tinubu Ya Binciki Buhari da Mutanensa

Jami’an Tsaro Sun Kama Mahdi da Ya Roki Tinubu Ya Binciki Buhari da Mutanensa

  • Lauyan da yake kare Mahdi Shehu ya fitar da sanarwa cewa ‘yan sanda sun cafke shi a garin Abuja
  • Fitaccen ‘dan kasuwan mai sharhi a kan siyasa ya shiga hannu ne bayan an rubuta korafi a kan shi
  • Abubakar Malami ya jefi Mahdi da neman kudi a hannun shi, lauyan attajirin ya musanya batun

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Maganar da ake yi, ana zargin jami’an tsaro sun yi ram da Mahdi Shehu wanda ya yi fice wajen gwagwarmaya a Najeriya.

Malam Mahdi Shehu wanda ya saba bankado sirri da tonon silili yana hannun ‘yan sanda kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto.

Mahdi
'Yan sanda sun kama Mahdi Shehu Hoto: Rescue Nigeria Urgently/Getty (Hoton nan bai da alaka da labarin)
Asali: Facebook

An cafke Mahdi Shehu a Abuja

Kara karanta wannan

Zanga-zanga sun tada hankalin Gwamnati, Shugaban kasa ya dauki mataki a guje

Lauyan ‘dan kasuwan, M. I. Abubakar esq ya shaida cewa jami’an ‘yan sanda sun kama shi a dalilin kiran da ya yi ga Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahdi Shehu ya nemi shugaba Bola Tinubu ya binciki tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu manyan jami’ansa.

Lauyan ya ce dakarun Sufetan ‘yan sanda na kasa sun tsare Mahdi bayan wani korafi da tsohon AGF, Abubakar Malami SAN ya rubuta.

Mahdi Shehu da Abubakar Malami

Sahara Reporters ta kawo labarin, ta ce an tsare shugaban kamfanin na Dialogue a Abuja. Ba a yau Mahdi ya fara shiga matsala ba.

Abubakar Malami SAN yana cikin na kusa da shugaba Buhari, ya yi shekaru kusan takwas a minista har ya zama surukin mai gidansa.

A jawabin M. I Abubakar, 21st Century Chronicle ta ce an zargi Mahdi da neman tatsar N500m daga hannun tsohon ministan shari’ar.

Kara karanta wannan

Labari da dumi-dumi: Bola Tinubu ya shigo Najeriya bayan shafe makonni 2 a Faransa

Jawabin lauyan ya musanya hakan, yake cewa wanda yake karewa bai nemi sisi daga hannun Malami ko wani cikin danginsa ba.

Mahdi Shehu ya tsayawa Jim Obazee

A makon nan ne Mahdi ya fito shafin X da aka fi sani da Twitter, yana mai zargin wasu na kusa da Buhari da neman bata Jim Obazee.

Attajirin yana ganin ana kokarin lalata sunan Obazee ne saboda binciken da ya yi a CBN wanda ya jawo ake tuhumar Godwin Emefiele.

Irin bayanan Mahdi Shehu

Kamar yadda ya saba sharhi kan al'amuran jama'a, kwanaki aka ji labari Mahdi Shehu ya bankado bayanai kan hakin ma'adanai.

An ji shi yana cewa akwai wani haramtaccen wurin hakar zinare a Zamfara wanda tsohon gwamna, Sanata da Janar suka mallaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel