Mai Girkin Tsohon Gwamna Ya Shiga Matsala Bayan Wawushe Kayan Miliyoyin Ambode

Mai Girkin Tsohon Gwamna Ya Shiga Matsala Bayan Wawushe Kayan Miliyoyin Ambode

  • Amana ya yi karanci a zamanin yanzu bayan an tsare mai dafa abinci ga tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode kan zargin sata
  • Wanda ake zargin Abyomi Victor ya hada baki da wasu mutane inda suka sace kayayyaki na miliyoyin kudi a gidan tsohon gwamnan
  • Ana zargin Abayomi da aikata laifuffuka har guda biyu da suka hada da hadin baki da kuma sata da suka yi a gidan gwamnan da ke Ikoyi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas – Mai dafa abinci ga tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya shiga matsala bayan garkame shi a gidan kaso na tsawon kwanaki 30.

Ana zargin Victor Abayomi da satar kayayyakin tsohon gwamnan na miliyoyin kudi a gidansa da ke Ikoyi.

Kara karanta wannan

"Yadda Emefiele ya ba matarsa kwangilar biliyoyin Naira lokacin yana gwamnan CBN"

Kukun tsohon gwamna a APC ya shiga matsala kan zargin cin amanar mai gidansa
Ana zargin Abayomi da sace kayayyakin miliyoyin kudi a gidan Ambode da ke Legas. Hoto: @Akinwumiambode/Court of Appeal.
Asali: UGC

Wane umarni kotun ta bayar a Legas?

Mai Shari’a, Peter Nwaka da ke kotun Majistare a Yaba shi ya ba da wannan umarni a jiya Litinin 11 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Premium Times ta tattaro cewa wanda ake zargin ya na fuskantar tuhume-tuhume biyu da suka hada a hadin baki da kuma sata.

Lauyan hukumar DSS, Joshua Babalola ya fadawa kotun cewa Abayomi da wasu sun sace kayayyaki na miliyoyin kudi a gidan tsohon gwamnan da ke Ikoyi.

Yadda jami'an DSS suka kama Abayomi

Babalola ya ce jami’an DSS sun cafke Abayomi a ranar 7 ga watan Maris a karamar hukumar Molorundo da ke jihar Osun, cewar PM News.

Lauyan ya ce wannan laifi da Abayomi ya aikata ya sabawa sashe na 287 da kuma 411 na kundin laifuffukan jihar Legas.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba gwamnonin jihohi sabon umarni kan mafi karancin albashi, bayanai sun fito

Daga bisani alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraran karar har zuwa 8 ga watan Afrilun wannan shekara tare da umarnin ci gaba da bincike.

Mata ta fada cikin kogi a Legas

Kun ji cewa rundunar ‘yan sanda da sanar da cewa wata mata ta hallaka kanta bayan fadawa cikin kogi a jihar Legas.

Matar mai suna Folashade Nimotalahi ta yi tsalle ne inda ta fada cikin kogi daga cikin jirgin ruwa da ke tafiya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar haka a jiya Litinin 11 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel