Jam'iyyar APC
A labarin nan, za a ji yadda Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya koɗa tsohon Shugaban APC kuma tsohon gwamna a Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ya cika shekaru 76.
Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Barau I Jibrin ya taya tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, murnar cika shekaru 76 a duniya.
Mambobi 6 na majalisar dokokin Zamfara sun sauya sheka daga PDP zuwa APC, saboda rikice-rikicen cikin gida da dakatar da su da majalisa ta yi ba bisa ƙa'ida ba.
Nentawe Yilwatda, shugaban APC na kasa, ya nada mashawarta na musamman da mataimaka ciki har da Danladi Sankara domin inganta gudanarwar jam'iyyar a kasa.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, ya nuna damuwa kan sauya shekar da ake yi zuwa jam'iyya APC. Ya ce APC za ta ruguje.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ba Fa'izu Alfindiki Naira miliyan 7 bayan zargin Abba Kabir Yusuf da tauye masa hakki bayan gama aiki.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sallami hadimansa guda hudu nan take bisa dukan kansilan Shamaki da ya bayyana a bidiyo mai yawo.
Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya ce yana da cikakkiyar cancantar jagorantar Najeriya, tare da cewa ba zai goyi bayan Tinubu a 2027 ba. Ya yi gargadi kan rugujewar PDP.
Sanatoci biyu da ‘yan Majalisar Wakilai shida daga Rivers sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, suna danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da sauyin siyasa.
Jam'iyyar APC
Samu kari