Muhammadu Buhari
A labarin nan, za a ji yadda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tunatar da jama'a cewa su zama masu gaskiya, rikon amana kare abin ya rataya a wuyansu.
Muhammadu Buhari ya ce ba zai bar wa ‘ya’yansa dukiya ba, amma zai bar musu ilimi domin su zama masu dogaro da kai su kuma fuskanci rayuwa cikin ƙwarewa.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya aika da sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar tsohon shugaban kasan Najeriya, Alhaji Muhammadu Buhari.
Malamin addinin Musulunci, Dr Abdullahi Yankaba ya rasu a jihar Kano a yau Lititin, 14 ga Yuli. Malamin ya rasu ne ana tsaka da jimamin rasuwar Muhammadu Buhari.
A labarin nan, za ji cewa Sanatan Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya bayyana alhini a kan rashin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya rasu a Landan.
Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana kan alakar shi da marigayi Muhammadu Buhari a 1962 bayan shiga aikin soja tare.
Zahra Buhari ta balle da kuka a gaban asibitin London yayin da aka tabbatar da rasuwar mahaifinta, tsohon shugaban Najeriya, lamarin da ya girgiza ‘yan Najeriya.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ayyana ranar hutu don rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya yi addu'ar Allah ya yi masa rahama.
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rasu ya ce ya gudu ya shiga soja ne bayan ya gudu daga gida ya shiga soja saboda za a masa aure a Daura.
Muhammadu Buhari
Samu kari