Atiku Abubakar
Tsohuwar uwargidar shugaban kasa, Aiha Buhari da diyarta Hanan Buhari sun kai ziyarar bam girma ga Atiku Abubakar a masaukinsa a kasa mai tsarki.
Wani dan majalisar wakilai daga jihar Adamawa, Muhammad Basil, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ja baya da siyasa.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi magana kan karfin da jam'iyyun adawa suke da shi. Ya bayyana bambancin ADC da jam'iyyar APC.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi ganawar sirri da Sanata Abdulaziz Yari a Abuja. Wata majiyar ADC ta yi karin bayani kan ganawar.
Jam'iyyar APC ta yi martani mai zafi game da zargin da ake yi mata cewa tana tilasta ma'aikatan gwamnati shiga cikinta inda ta ke tuhumar ADC mai adawa.
Jagoran kungiyar Obidient na kasa, Yunusa Tanko Yakasai, ya bayyana cewa ya kamata Atiku Abubakar, ya marawa Peter Obi baya don zama shugaban kasa a 2027.
Peter Obi ya ce "matsayin lamba ɗaya" zai nema a zaɓen 2027, inda ya yi watsi da zama mataimakin Atiku ko Kwankwaso a jam'iyyar ADC yayin yakin neman zaɓen AMAC.
Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce matsalolin Najeriya ba talauci ne ya haddasa su ba, illa gazawar ’yan siyasa wajen tafiyar da albarkatun kasa yadda ya dace
Rabiu Musa Kwankwaso na jinkirta komawa ADC saboda rashin tabbacin tikitin Peter Obi na 2027, tare da shawarwari daga Arewa da Cif Olusegun Obasanjo.
Atiku Abubakar
Samu kari