Arewa
‘Yan fashi sama da 50 sun farmaki kwalejin tarayya ta Bauchi, inda suka jikkata dalibai 10, lamarin ya sanya hukumomi suka rufe makarantar gaba daya.
Wani jigo a jam'iyyar PDP ya bayyana amfanin da tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan zai yi wa Najeriya idan ya zama shugaba a karo na biyu.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal ya ce Arewa ta kafa kungiyar NPCP don zaben dan siyasar da zai magance matsalolin yankin tare da canza tsarin 2023.
Fursunoni 16 sun tsere daga gidan gyaran hali na Keffi, an ce an sake kama bakwai daga cikin su, yayin da shugaban NCoS ya sha alwashin hukunta masu hannu a lamarin.
Majiyoyi sun ce karamar hukumar Safana a jihar Katsina ta kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga, kamar Jibia, Batsari, da Danmusa, domin zaman lafiya.
NiMet ta yi hasashen ambaliya a Adamawa, Taraba da Benue saboda mamakon ruwan sama, ta bukaci mazauna da hukumomi su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyi.
Kungiyar NUP ta Arewa ta ce jihohi 4 daga 19 na Arewa ke biyan mafi ƙarancin fansho na N32,000, yayin da wasu ke biyan N3,000 zuwa N5,000 ga tsofaffin ma'aikata.
Fasahar zamani ta rusa sana’o’in gargajiya kamar sayar da kaset, DVD, gyaran rediyo, ɗaukar hoto, yayin da wayar zamani ta mamaye rayuwa da harkokin yau da kullum.
Rahotanni sun tabbatar mana da cewa rikicin da ya barke tsakanin Dogo Gide da Kachalla Alti a Tsafe, Zamfara, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da sace wasu shida
Arewa
Samu kari