Arewa
Hukumar NiMET ta gargadi mazauna wasu jihohi shida na Arewacin Najeriya da su shirya ganin ruwan sama mai hade da tsawa da iska mai karfi a kwanaki masu zuwa.
Gwamnatin tarayya ta ce mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa ya kashe akalla mutane 49 a jihohin Taraba, Adamawa da Jigawa,ana fargabar karuwar ambaliya.
Ana zargin hakimin da ke kula da wasu yankuna a jihar Kano wanda Sarki Sanusi II ya nada shi ya sallami dagatai guda uku daga sarauta da ake ganin ya saba ka'ida.
A ranar 26 ga watan Agusta ake murnar ranar Hausa a duniya. Legit Hausa ta tattaro muku hukuncin ranar Hausa a Musulunci, muhimmancin koyon ka'idojin rubutun Hausa
Kwamishinan kudi na jihar Borno, Ahmed Ali Ahmed ya kwanta dama. An ce ya rasu ne a safiyar yau Litinin, 26 ga Agustan 2024 a cikin gidansa da ke Maiduguri.
Wasu yan bindiga sun sace hakimin Garu Kurama, Yakubu Jadi da wasu mutane shida a kauyen Gurzan Kurama da ke Kaduna ta Kudu a daren ranar Juma'a da ta gabata.
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaɗu bayan rashin da ya tafka na kaninsa, Alhaji Ahmad Ibrahim Tambuwal a jiya Asabar 24 ga watan Agustan 2024 a birnin Abuja.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya shirya gudanar da wani babban taro kan fasaha da kirkire-kirkire a Arewacin Najeriya yayin da zai kaddamar da kamfaninsa.
Jami'an tsaro sun yi nasarar cafke wasu kasurguman yan bindiga da ke karkashin jagorancin rikakken dan ta'adda, Bello Turji a jihar Sokoto yayin wani samame.
Arewa
Samu kari