Abuja
Hukumar NEMA ta ce mutum 236 sun mutu a ambaliyar ruwa da ta shafi jihohi 27 da Abuja, yayin da fiye da 400,000 suka rasa gidaje da gonaki a fadin kasa.
Hasashen yanayin ya nuna cewa za a samu ruwan sama a wasu jihohin Arewa, ciki har da Taraba, Kebbi, da sauransu, yayin da damina ke bankwana a gobe Litinin.
Minista Imaan Sulaiman-Ibrahim ta ce auren wuri yana hana ci gaban Najeriya, inda 44% na ‘yan mata ke yin aure kafin shekara 18, bisa bayanan hukumar UNICEF.
Kungiyar malaman jami'o'i, ASUU ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu a duk jami’o’in gwamnati daga Litinin, 13 ga Oktobar 2025 yayin taro a Abuja.
Shugaba Bola Tinubu zai halarci taron Aqaba Process a Rome, Italiya, don tattauna matsalar tsaro a yammacin Afirka da dabarun haɗin kai wajen yakar ta’addanci
EFCC ta gurfanar da tsohuwar shugabar NSITF, Ngozi Olejeme, kan tuhumar karkatar da N1bn da dala miliyan biyu; sai dai Ngozi ta ki amincewa da wannan tuhuma.
Majiyoyinmu sun tabbatar da cewa an samu gawar babban dan sanda, ASP Cyril Takim mai shekaru 54 bayan ya fadi a bandakinsa a Mararaba da ke Nasarawa.
Bayan soke digiri dan Kotono a wasu jami'o'in Benin da sun fito da dabarar shiga shirin NYSC bayan gwamnatin Najeriya ta soke jami'o'in da suke karatu a ketare.
Ministan ma'adanai, Dele Alake ya nunka tsaronsa bayan samun barazanar kisa daga wadanda aka soke wa lasisin hakar ma’adinai, duk da umarnin Shugaba Tinubu.
Abuja
Samu kari