FCT: An Tafka Ɓarna Yayin da Mutane Ke Tsaka da Sallar Tarawihi a Watan Azumin Ramadan

FCT: An Tafka Ɓarna Yayin da Mutane Ke Tsaka da Sallar Tarawihi a Watan Azumin Ramadan

  • Wasu ɓarayi sun sace baburan mutane yayin da ake tsaka da sallar tarawihi da daren ranar Asabar a Paso da ke birnin Abuja
  • Wani mazaunin yankin, Mika'il Abdulsalam, ya ce tun farkon Ramadan ake zuwa da baburan masallacin amma sai asabar aka ɗauke su
  • Wani ɗan banga ya ce suna kan aikin kwato baburan, amma rundunar ƴan sanda ba ta ce komai ba kawo yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rahotanni sun nuna cewa wasu da ake kyautata zaton ɓarayi ne sun sace babura biyu a babban masallacin Paso da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada a Abuja.

Lamarin dai ya auku ne yayin da al'ummar Musulmi ke tsaka da sallar Taraweeh domin neman lada a watan azumin Ramadan.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan 'yan bindiga sun hallaka babban malamin addini a wani sabon hari

Yan sanda.
Barayi Sun Tafka Barna a Masallaci Ana Tsaka da Sallah a Birnin Abuja Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Barayi sun yi sata cikin Ramadan a Abuja

Wani mazaunin Paso, Mikail Abdulsalam, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar Daily Trust ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa an sace baburan ne ranar Asabar da misalin karfe 8:29 na dare a lokacin da musulmi suke gudanar da sallar tarawihi a babban masallacin kauyen.

Abdulsalam ya ce miyagun da ake zargin ɓarayin babura ne sun ɓalle makullan baburan da ƙarfin tuwo, kana suka yi awon gaba da su bayan an sha ruwa.

Yadda baburan suka ɓata a Masallaci

Ya ce masu baburan guda biyu, Lawali da Dahiru, sun ankarar da mutane abinda ya faru a lokacin da suka fito daga Masallaci, suka nemi baburansu a wurin da suƙa aje suka rasa.

Mutumin ya ce:

"Tun da aka fara azumin Ramadan masu baburan ke zuwa da su Masallaci domin yin sallar tarawihi a cikin jam'i kowace rana a babban Masallacin.

Kara karanta wannan

Shugabannin APC sun faɗawa Tinubu mataki 1 da ya kamata ya ɗauka kan wasu hafsoshin tsaro a Najeriya

"A ranar Asabar bayan kammala sallar suka ankarar da jama'a cewa ba su ga baburansu ba."

Wane mataki aka ɗauka?

Wani dan banga a yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa babura biyu sun ɓata lokacin Sallar tarawihi a yankin Paso ranar Asabar.

Jami'in ɗan bangan ya ƙara da cewa suna iya bakin kokarinsu domin binciko ɓarayin da kuma kwato baburan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, Adeh Josephine, ba ta amsa sakon salula da aka tura mata kan lamarin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Ramadan: Matashi ya turawa mahaifiyarsa kyauta

A wani rahoton kuma Wani faifan bidiyo ya nuna irin shaukin da wani matashi ya jefa mahaifiyarsa a ciki bayan da ya aika mata kudi a matsayin kyautar watan Ramadan.

Mahaifiyar ta nuna matukar jin dadinta akan abin da danta ya yi ta hanyar aika masa da sakon murya mai tsuma zuciya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel