Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Ambasada Bawa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Abuja, Bayanai Sun Fito

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Ambasada Bawa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Abuja, Bayanai Sun Fito

  • Jakadan kasar Ghana a Najeriya, Rawhide Bawa ya rasu a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024
  • Wata majiya ta bayyana cewa duk da ma'aikatar kasashen waje ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba amma an sanar da ita abinda ya faru
  • Wasu bayanai sun nuna cewa an kai gawar marigayi Bawa zuwa kasarsa Ghana domin yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jakadan ƙasar Ghana a Najeriya, Ambasada Rawhide Bawa, ya riga mu gidan gaskiya yayin da al'ummar Musulmai na duniya ke ibadar azumin watan Ramadan.

Ambasada Bawa ya rasu ne a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

Ambasada Bawa na ƙasar Ghana.
Allah ya yi wa ambasadan kasar Ghana a Najeriya rasuwa Hoto: Facebook
Asali: UGC

Tuni dai aka kai gawar jami’in diflomasiyyar mai shekaru 65 zuwa ƙasar Ghana domin yi masa jana’iza, tare da bin ka’idojin da addinin Musulunci ya tanada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har kawo yanzu dai ma'aikatar ƙasashen waje ta Najeriya ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan wannan mutuwa ta jakadan kasar Ghana ba.

Amma wata majiya ta tabbatar da cewa an sanar da ma'aikatar labarin rasuwar Bawa.

Sarkin kasar Ibadan ya kwanta dama

Wannan na zuwa ne yayin da ake jimamin rasuwar babban sarkin kasar Ibadan, Olubadan watau Oba Leka Balogun, wanda ya rasu yana da shekaru 82 a duniya.

Basaraken ya rasu ne ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, 2024 kwanaki kalilan bayan ya yi bikin cika shekaru biyu a kan karagar mulki.

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya tabbatar da wannan babban rashi da aka yi a jiharsa a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa ya fitar.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Rundunar soji ta saduda, ta nemi agajin EFCC a wasu bangarori, ta fadi dalili

Tuni dai aka yi jana'izar marigayi Oba Balogun kamar yadda addinin musulunci ya tanada ranar Jumu'a da ta gabata.

NEF ta tsoma baki kan bukatar Sheikh Gumi

A wani rahoton kuma Dattawan Arewa sun buƙaci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Sheikh Gumi damar tattauanawa da ƴan bindigan da suka sace ɗalibai a Kaduna.

Kungiyar dattawan NEF ta bayyana goyon bayanta ga yunkurin Gumi na shiga tsakani da ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel