Bola Tinubu
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na samun goyon baya kan 2027 ne saboda ayyukansa.
Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya ce matuƙar PDP ta rushe to Najeriya za ta shiga babbar matsala domin za a samu shugaban kasa ɗan kama karya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi izinin majalisa wajen ciwo bashin dala biliyan 21.5 daga ketare. Tinubu ya ce za a yi ayyukan raya kasa da kudin a Najeriya.
A labarin nan, za ku ji yadda ayyukan Bola Ahmed Tinubu suka farantawa matasan jihar Kaduna, kuma sun dauki alkawarin saka masa a babban zaben 2027.
Za a ji yadda rikicin SDP ya tsananta yayin da wani bangare ya yi watsi da Shehu Gabam tare da goyon bayan Cif Adedina a matsayin shugaban jam’iyyar.
Tsohon ministan shari'a a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, Abubakar Malami ya soki Bola Tinubu, gwamnonin APC da Ganduje kan mayar da hankali a 2027.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi magana a ranar yara ta 2025 inda ya ce za a tabbatar da kare yara daga cin zarafi da musguna musu. Ya ce za inganta rayuwar yara.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dele Momodu ya yabawa Bola Tinubu da ya takawa Nyesom Wike birki kan rufe ofishin PDP da wasu wurare a birnin tarayya.
Za a ji Gwamna Babagana Zulum ya gana da Tinubu a Abuja kan tsaro, ya ce ba zai bari Boko Haram da ISWAP su mamaye kowace ƙaramar hukuma a Borno ba.
Bola Tinubu
Samu kari