Majalisar dokokin tarayya
Shugaban jam'iyyar Labour Party na kasa ya kore yuwuwar zababbun Sanatoci da mambobin majalisar wakilan tarayya na jam'iyyar su sauya sheƙa bayan rantsar da su.
Dan majalisar wakilai daga jihar Oyo, Akin Alabi ya bayyana cewa kirista daga kudu maso gabas ko kudu maso kudu ne ya kamata ya zama shugaban majalisar dattawa.
Bulaliyar majalisar dattawa, Orji Kalu, ya ce zai ajiye kudrinsa na son zama shugaban majalisar dattawa idan zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi haka.
Rotimi Akeredolu da Yahaya Bello za su goyi bayan takarar Ahmed Idris Wase a Majalisar Wakilai, sun rabu da Abbas Tajuddeen wanda shi ne 'Dan takarar El-Rufai
Yanzu muke samun labarin rasuwar wani tsohon dan majalisar wakilai a jihar Imo, inda aka ce ya yi jinyar cutar daji kafin daga bisani ya rasu a ranar Litinin.
Barau Ibrahim Jibrin ya shiga sahun wadanda za su nemi shugabancin Majalisar Dattawa. Da yiwuwar Sanatan Arewacin Kano ya gwabza da Orji Uzor Kalu a takarar.
Mai dakin Gwamna na Ekiti ta yi kira ga mutanen jihar da su cigaba da ba Gwamnatin mijinta bayan ganin 23% na kujerun Majalisa sun shiga hannun mata a Ekiti.
Za a samu matasa a majalisun dokoki, ‘Yan shekara 26 zuwa 30 sun yi nasara a Kwara, Yobe, Ogun, Shugaban majalisar Yobe ya rasa kujerarsa ga ‘Dan shekara 34.
‘Yan Majalisa da yawa sun rasa Kujerunsu a 2023. Shugaban majalisar wakilan tarayyan Femi Gbajabiamila ya zargi masu zabe da amfani da addini da kabilanci.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari