Yan ta'adda
'Yan ta'addan da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sace mata 12 a jihar Borno. Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa tana kokarin ceto matan da aka sace.
Jam'iyyar PDP ta soki rufe makarantu da gwamnati ta yi saboda sace-sacen dalibai, ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya nemi taimako ko ya yi murabus idan ba zai iya ba.
Masu garkuwa da mutane sun kai hari a Toro, Bauchi, inda suka kashe dan agajin Izalah, Alhaji Muhammad Bakoshi, sannan suka sace matarsa da ‘yarsa mai shekara biyar.
Yara sun fara barin FGGC Bwari bayan umarnin gwamnati na rufe makarantu 47 saboda barazanar tsaro da yawaitar sace dalibai a Arewa. Iyaye sun yi martani kan hakan.
Sanatan Kebbi ta Kudu a majalisar dattawa, Garba Maidoki ya bayyana bakin cikinsa kan sace dalibai a Maga a jihar yana cewa lamarin ya taba masa zuciya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an goge shafin Facebook na Fasto Ezekiel Dachomo yayin da ake cece-kuce kan kalamansa game da kisan Kiristoci a Najeriya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya damu matukan kan matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya. Ya ce gwamnatinsa na daukar matakai.
Gwamna Zulum ya umurci mazauna Borno su gudanar da azumi da addu’a a Litinin domin neman taimakon Allah kan sabon tashin hankali da ake fuskanta a jihar.
A labarin nan, za a ji gwamnatin Nasir Idris ta Kebbi ta yi bayani a kan lokacin da ta ke sa ran jami'an tsaro za su samu nasarar ƙwato ƴan matan makarantar Maga.
Yan ta'adda
Samu kari