Yan ta'adda
Yayin da ta'addanci ke kara ƙamari, Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta binciki kudin da ake taimakon Boko Haram.
Sanata Ali Ndume ya ziyarci dakarun sojojin Najeriya da suka kashe 'yan boko Haram da dama. Ya raba tallafi ga mutanen mazabarsa da harin ya shafa.
Harin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai kan sansanin sojoji a jihar Borno ya jawo asarar rayukan jami'an tsaro masu yawa. An nemi wasu daga ciki an rasa.
Gwamna Makinde ya gargadi al'umma kan yaduwar 'yan bindiga da aka koro daga Arewa maso Yamma. Gwamnan ya nemi hadin kan sarakuna da al'ummar jihar.
Gwamnan Jihar Oyo ya ce 'yan bindiga sun fara fadada ta'addanci wajen kaura da Arewa maso Yamma zuwa jihar Oyo. Ya ce za a yaki 'yan ta'addar da gaske.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai mummunan hari gidan wani boka a Anambra sun kashe masa yara uku sun wurga su a cikin wata mota. An fara bincike.
ISWAP ta kai hari kan sansanin soja a Damboa, ta kashe sojoji shida, ta banka wa sansanin wuta. Rikicin na tun 2009 ya halaka mutane 40,000 da raba miliyan biyu.
Sojojin Najeriya sun bayyana cewa Bello Turji yana buya a ramuka kamar beran daji sakamakon farmaki da suke kai masa ta sama da kasa a yankin Shinkafi.
Gwamnatin jihar Neja ta gargadi mazauna wasu yankunan jihar kan su guji zuwa gonakinsu domin gujewa taka ababe masu fashewa da 'yan ta'adda suka binne.
Yan ta'adda
Samu kari