Yan ta'adda
Alkalin babbar kotun jihar Borno da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da shi, Haruna Mshelia, ya kubuta. Alkalin ya kubuta ne bayan ta kwashe watanni biyu a tsare.
Rundunar sojojin Najeriya a Jalingo ta ce ta samu nasarar kama wata matashiya da ke kaiwa 'yan bindiga bayanai kuma ana zargin budurwar dan bindiga 'Chen' ce.
Rahotanni sun bayyana cewa an cimma matsaya tsakanin mazauna kauyen Moriki da ke Zamfara da Bello Turji cewa 'yan kauye za su biya diyyar N30m na kashe shanunsa.
Rahoto ya bayyana cewa kimanin mutane 13,346 aka kashe yayin da aka sace wasu 9,207 daga hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki zuwa watan Satumbar 2024.
Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa sojoji sun samu nasarar kashe miyagun ƴan ta'adda 152, sun kama wasu 109 tare da ceto mutane 91 a mako guda.
A rahoton nan,za ku ji cewa kungiyar North West Agenda for Peace (NOWAP) ta bayyana fatan gwamnatin tarayya za ta kawo karshen matsalar tsaro a yankin.
A wannan rahoton, gwamnatin jihar Zamfara ta nesanta kanta da sanarwar da aka ce ta fito daga gare ta na shirin tattaunawa da yan ta'adda domin sulhu a jihar.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da kimanin mutane 15 a wani sabon hari da suka kai garin Mani da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Yan bindiga sun fara saka mutane bauta a Areacin Najeriya. Yan bindiga sun fara saka mutane noma a gonakinsu. Suna kuma kwace amfanin gonar mutane.
Yan ta'adda
Samu kari