Mafi karancin albashi
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Katsina ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin jihar kan sabon mafi karancin albashi na ma'aikata.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da sabon mafi karancin albashi gama'aikatan jihar. Gwamnan ya amince a fara biyan sabon albashin daga watan Disamba.
Gwamnatin Anambra ta musanta wani rahoto da ke yawo wanda ya cire jihar daga jerin waɗanda suka yi ƙarin albashi, ta ce tun a watan Oktoba aka fara biya.
Kungiyar kwadago ta ƙasa watau NLC ta ce wa'adin da ta ba gwamnatocin jihohi kan fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi yana nan daram, ta ce ba abin da ya sauya.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da yi wa likitoci karin albashi a jihar. Gwamna Zulum ya amince a rika biyansu daidai da na tarayya.
Kungiyar 'yan kwadago a Zamfara ta yi barazanar tsuduma yajin aiki idan gwamnatin jiharba ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi zuwa karshen Nuwamba ba.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya amince da N75,000 a matsayin sabon albashi mafi kankanta da gwamnatinsa za ta fara biyan ma'aikata nan ba da daɗewa ba.
Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Biodun Oyebanji ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati, ya ce har ƴan fansho za su ga canji.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya amince da biyan N70,000 ga ma'aikatan birnin Tarayya Abuja domin ragewa ma'aikatan halin tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya.
Mafi karancin albashi
Samu kari