Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Ogun Ya Bayyana Yadda Ya Sha Da Kyar a Hannun 'Yan Daba

Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Ogun Ya Bayyana Yadda Ya Sha Da Kyar a Hannun 'Yan Daba

  • Segun Showunmi, tsohon ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Ogun, ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya a hannun ƴan daba
  • Ƴan daba dai sun farmaki jigon na jam'iyyar PDP lokacin da ya ke ƙoƙarin shigar harabar kotu inda ake sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar
  • Ya bayyana cewa ya samu ya tsira daga hannun ƴan daban amma fa ya samu tabo sosai saboda harin da aka kai masa

Ogun, Abeokuta - Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Ogun, ya bayyana baƙar wuyar da ya sha a hannun ƴan daba wajen shiga harabar kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar.

Wasu ƴan daba dai sun farmaki Showunmi yayin da ya ke ƙoƙarin shiga harabar kotun domin halartar zaman sauraron ƙarar na farko.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

Dan takarar gwamnan PDP a jihar Ogun ya sha da kyar a hannun 'yan bindiga
Segun ya nemi a mayar da sauraron karar zuwa Abuja Hoto: Segun Showunmi
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ambato Showunmi na roƙon a mayar da sauraron ƙarar zuwa birnin tarayya Abuja, bisa barazanar tsaron da ake fama da ita.

Yadda ya tsira daga hannunsu

Tsohon ɗan takarar a yayin ganawa da manema labarai, ya ce ya taki sa'a ya tsira daga harin amma an yi masa tabo sosai a jikinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Premium Times ta rahoto tsohon ɗan takarar gwamnan na cewa:

"A taimaka a mayar da sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Ogun zuwa Abuja saboda babu tsaro, ta yadda za mu iya zuwa mu saurari ƙarar cikin natsuwa ta yadda kowa zai san yadda shari'a ke wakana, da sanin abin yi bayan an kammala hukunci."
"Rana ce wacce aka tafka abin kunya, rana ce wacce babu wani mai hankali ɗan jihar Ogun da zai yi alfahari da abinda aka yi. A yanzu haka wasu daga cikin magoya baya na suna asibiti ana duba lafiyarsu."

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Abdul'aziz Yari Ya Samu Gagarumar Nasara a Kotu Dab Da Zaben Shugaban Majalisa

"Cikin sa'a na samu na tsira na fita daga wajen, amma fa na ji a jikina."

Yan Daba Sun Lakada Wa Dan Takarar Gwamnan PDP Duka a Wajen Kotu

A baya rahoto ya zo kan yadda ƴan daban siyasa suka lakadawa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP, dukan tsiya a harabar kotu.

Segun Showunmi ya ga ta kansa bayan ƴan daba ɗauke da sanduna da bulali sun farmake shi a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel