Ba na shan giya ko taba amma ina da son motoci - Dino Melaye

Ba na shan giya ko taba amma ina da son motoci - Dino Melaye

- Dino Melaye ya bayyana abin da ya sa yake hawa manyan motoci

- Sanatan yace kowa dai akwai abin da yake sha'awa a rayuwar sa

- 'Dan Majalisar yace ba abin da yake so irin manyan motocin nan

Fitaccen 'Dan Majalisar kasar nan Sanata Dino Melaye ya bayyana abin da ya sa yake hawa manyan motoci masu tsada duk da yana ikirarin cewa shi fa mutumin Talakawa ne kuma hakkin su yake nema masu a Najeriya.

Ba na shan giya ko taba amma ina da son motoci - Dino Melaye
Dino Melaye yace shi abin da yake so a rayuwa su ne motoci

Dino Melaye yayi hira da BBC Hausa kwanaki inda aka tambaye sa game da rayuwar da yake yi ta kasaita da wadata da alfarma. Sanatan yace babu hadisi ko Annabin da ya hana a ji dadi a more rayuwa da dukiyar halal.

KU KARANTA: Wasu ayyuka da Sojojin Najeriya su kayi a Jihar Legas

Sanata Melaye ya bayyana cewa da arzikin da Allah ya ba shi wanda ba sata yayi ba yake sayen motoci. Sanatan yace har yau ana binciken sa kuma ba a taba samun sa da laifin sata ba don haka ya zabi ya hau mota da kudin sa.

'Dan Majalisar na Yankin Kogi yace ba ya shan giya ko sigari amma dai yana da sha'awar motoci a matsayin sa na mutum inda yace kwanan nan ma zai sayo wata. Sanatan yace ba sata yayi ba kuma arziki Ubangiji ne ya mallaka masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng