Jerin manyan mutanen da su ke dauke da kwayar cutar COVID-19 a Yau
Akalla mutane 97 ne ake da labarin su na dauke da cutar COVID-19 a Ranar 28 ga Watan Maris 2020, kamar yadda hukumar NCDC mai takaita yaduwar cututtuka ta bayyana.
Kawo yanzu an yi wa mutane fiye da 150 gwaji a Najeriya, inda aka tabbatar da cewa an samu mutane 97 da su ka kamu da wannan cuta ta COVID-19 mai hana numfashi.
Daga cikin shaharrun wadanda aka tabbatar sun kamu da wannan cuta akwai:
1. Abba Kyari
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya kamu da wannan cuta bayan wasu tafiye-tafiye da ya yi zuwa Jamus da wasu kasashe. Ana tunanin cewa Kyari ya na jinya a asibiti.
2. Bala Abdulkadir Mohammed
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya na cikin wadanda wannan cuta ta yi wa kamu a Najeriya. Gwamnan ya hadu da Mohammed Atiku, kuma ya fita ziyara kasar waje kwanaki.
3. Nasir El-Rufai
A Ranar 28 ga Watan Maris, gwamnnan Kaduna Nasir El-Rufai ya tabbatarwa mutanen jiharsa cewa ya kamu da Coronavirus. Hakan na zuwa ne bayan gwamnan ya dauki matakin kare jihar.
KU KARANTA: Ban dauke da kwayar cutar Coronavirus - Garba Shehu
4. Mohammed Atiku Abubakar
Alhaji Mohammed Atiku Abubakar ya na dauke da cutar COVID-19. Mahaifinsa, Atiku Abubakar, ya tabbatar da cewa ‘Dansa ya kamu, amma ana kula da shi a asibitin Gwagwalada da ke Abuja.
5. Abokan Bala Mohammed
Daga cikin na-kusa da gwamnan Bauchi, akwai wani Amininsa mai shekaru 62 da ya kamu da wannan cuta. Gwamnatin jihar Bauchi ba ta bayyanawa kowa sunan wannan Bawan Allah ba.
6. Chioma Rowland
Shararren Mawaki Davido, ya bayyana cewa Mahaifiyar ‘Dansa kuma wanda zai aura, Chioma Rowland ta kamu da cutar COVID-19. Chioma ta bayyana wannan da kanta a shafin Tuwita.
7. Suleiman Achimugu
Injiniya Suleiman Achimugu ya na cikin wadanda su ka fara kamuwa da COVID-19 bayan zuwansa Ingila. Tun a makon jiya cutar ta kashe tsohon shugaban hukumar PPMC na kasa.
8. Muhammed Babandede
Shugaban hukumar da ke kula da shige da fice a Najeriya, Muhammed Babandede ya kamu da wannan cuta. Babandede ya shaidawa ‘Yan jarida wannan ta WhatsApp a karshen makon nan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng