Waziri: Tsohon Minista Ya Fice daga PDP, Ya Shiga Jam'iyyar ADC

Waziri: Tsohon Minista Ya Fice daga PDP, Ya Shiga Jam'iyyar ADC

  • Adamu Waziri, daya daga cikin wadanda suka kafa PDP kuma mamba a kwamitin amintattu (BoT), ya fice daga jam’iyyar, ya koma ADC
  • Ya ce ya fice daga PDP ne saboda yadda ya damu da wahalar da 'yan Najeriya ke fuskanta da kuma rashin karfin PDP a fannin adawa
  • Adamu Waziri ya bayyana cewa jam'iyyar ADC tana da ikon kwace mulki daga APC a 2027 don dawo da martabar tattalin arziƙin Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yobe – Daya daga cikin wadanda suka assasa PDP kuma mamba a kwamitin amintattu, Adamu Waziri, ya yi murabus daga jam’iyyar.

Adamu Waziri, wanda tsohon ministan harkokin ‘yan sanda ne ya koma jam’iyyar hadaka ta ADC bayan barin PDP a karshen makon jiya.

Tsohon ministan harkokin 'yan sanda, Adamu Waziri ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa ADC
Adamu Waziri ya jagoranci daruruwan magoya bayansa zuwa ADC bayan barin PDP a Yobe. Hoto: Abakar Moi Akko
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Adamu Waziri ya sanar da matakin murabus din nasa da komawa ADC a mazabarsa ta Dogo Tebo da ke Potiskum, jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Yaƴan jagororin ADC da ke cikin jam'iyyun APC da PDP a yau

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya ce matakin ya yi daidai da kundin tsarin mulkin PDP, wanda ke buƙatar yin murabus a hukumance a matakin mazaba.

Dalilin Adamu Waziri na barin jam'iyyar PDP

Adamu Waziri ya ce matakin nasa ya biyo bayan “tattaunawa mai zurfi da kuma tunani na kashin kai,” yana mai jaddada cewa ba ya bar PDP saboda yana fushi da ita ba ne.

Dattijon ya ce kishin Najeriya da kuma damuwa game da wahalar da mutanen kasar ke fuskanta a kullum ne ya sa shi barin PDP don hada kai da masu son kawo canji.

Yayin da yake bayanin matakin nasa, Adamu Waziri ya ce PDP ta sauka daga matsayin jam'iyyar adawa mafi karfi a yanzu.

“Ni mamba ne na PDP, mu ne muka kafa jam'iyyar, amma saboda halin da ake ciki da kuma maslahar al’umma, na yanke shawarar yin murabus.
“Rashin tsaro ya mamaye gidajenmu, musamman a Arewacin Najeriya, Boko Haram, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ta’addanci sun zama wani ɓangare na rayuwarmu yayin da gwamnati ke fifita siyasa fiye da tsaron ‘yan ƙasarta."

Kara karanta wannan

'Zuwansa alheri ne': Ribadu ya faɗi yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa

- Waziri Adamu.

Matsayar Adamu Waziri kan jam'iyyar ADC

Ya buƙaci mabiyansa da su bi shi wajen tallafa wa kungiyar hadakar 'yan adawa da za ta iya ƙarfafa dimokuraɗiyya da kuma tabbatar da ingantaccen shugabanci.

Adamu Waziri ya bayyana matakin a matsayin mai wahala amma wanda ya zama wajibi, yana mai cewa shugabancin PDP na yanzu ya rasa alkibla.

“Lokacin da Cif Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar suka yi mulki daga 1999 zuwa 2007, an rage bashin Najeriya zuwa sifili, tattalin arziki ya bunƙasa kuma ‘yan Najeriya sun ji daɗin gwamnati fiye da yanzu,” in ji shi.

Ya nuna kwarin gwiwa cewa jam'iyyar ADC tana da ikon kwace mulki daga APC a 2027 kuma ta dawo da martabar tattalin arzikin Najeriya, inji rahoton jaridar Leadership.

Adamu Waziri ya ce yana da yakinin cewa jam'iyyar ADC za ta kwace mulki daga hannun APC a zaben 2027
Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Peter Obi da sauran 'yan adawa sun amince da shiga jam'iyyar ADC. Hoto: @ADCngcoalition
Source: Twitter

Martanin PDP kan murabus din Adamu Waziri

A martanin da ya mayar, shugaban PDP na mazabar Dogo Tebo, Muhammad Bomai, ya ce ya karɓi murabus ɗin Adamu Waziri cike da baƙin ciki, inda ya kira shi ginshiƙin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Tinubu na kan siraɗi da tsohon shugaban kwamitin sulhu na PDP ya haɗe da Atiku a ADC

“Adamu Waziri ya kasance wani babban jigo a cikin PDP, kuma za mu ji rashinsa sosai,” inji Muhammad Bomai.

Bomai ya kuma sanar da murabus dinsa daga PDP da kuma sauya shekarsa nan take zuwa ADC, yana mai cewa yana goyon bayan hangen nesan Waziri na samar da ingantacciyar Najeriya.

2027: Primate Ayodele ya hango makomar Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa, malamin Kirista, Primate Ayodele, ya ce Atiku Abubakar ne zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC a 2027, ba Peter Obi ba.

Ya yi kashedi ga jam’iyyar APC kan yiwuwar faduwa zabe a 2027 idan shugabanninta suka ƙi bin shawararsa, tare da nuna damuwa game da makomar jam’iyyar.

A gefe guda, Festus Keyamo ya zargi tawagar Atiku da yunƙurin amfani da Peter Obi don jawo ƙuri’u a zaben 2027 ba tare da tunanin ba shi tikiti ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com