Tinubu: Rarara Ya Ce ko Shi zai Kayar da Atiku, El Rufa'i da 'Yan ADC a 2027
- Dauda Kahutu Rarara ya ce ko shi ma idan ya tsaya takara zai iya kayar da 'yan adawa gaba ɗaya a zaɓen 2027 mai zuwa
- Mawakin ya zargi shugabannin haɗaka a ADC da gazawa, yana mai cewa talakawa ba za su sake amincewa da su ba
- Kahutu Rarara ya kare Bola Tinubu, yana mai cewa ya gaji kasar da Muhammadu Buhari ya lalata tun da ya rufe iyakoki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano - Mawakin siyasa mai goyon bayan jam’iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara, ya ya ce shi ma yana da damar tsayawa takara a 2027 kuma zai iya kayar da manyan ‘yan takarar haɗakar ADC.
A cewarsa, idan suna da abin da za su faɗa wa talakawa domin su jefa musu ƙuri’a, to shi ma yana da abin da zai faɗa da ya fi tasiri, kuma ya fi ƙarfinsu.

Source: Facebook
Rarara ya fadi haka ne a hirar da ya yi da DCL Hausa, inda ya ce su Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa’i, Rotimi Amaechi da sauran ‘yan adawa sun gaza tabuka komai a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rarara ya ce zai iya kayar da ADC
Da yake bayani, Rarara ya ce shi ma dan Najeriya ne, kuma yana da ‘yancin tsayawa takara kamar sauran manyan ‘yan siyasa.
Ya ce:
"Ni kaina idan na tsaya takara zan iya kayar da su, ko Atiku, ko El-Rufa’i ko Rotimi, balle kuma su ce za su kara da Bola Tinubu.”
A cewarsa, ‘yan adawa ba za su iya bayyana wani abin kwarai da suka yi a baya ba da zai sa a amince da su a 2027.
Rarara: "Masu haɗaka ba za su yi nasara ba"
Rarara ya bayyana taron hadakar ADC a matsayin “yu yu yu” mara amfani, yana mai cewa ba za su iya sauya siyasar 2027 ba.
Baya ga haka, mawakin ya zargi shugabannin adawa da gazawa lokacin da aka ba su dama a baya.
Ya ce talakawa ba mahaukata ba ne, sun ga lokacin da suka samu dama, amma ba su yi abin kirki ba.
Rarara ya ƙara da cewa shugaban kasa Tinubu yana aiki don gyara barnar da wasu daga cikin shugabannin da ke cikin haɗakar suka haifar.

Source: Twitter
“Laifin Buhari ne, ba na Tinubu ba,” Rarara
A kan zargin nuna kabilanci da ake yi wa Tinubu, Rarara ya ce laifin ba nasa ba ne, illa dai sakamakon abubuwan da suka faru a mulkin Muhammadu Buhari.
Ya ce rufe iyakoki da gazawar tsaro da aka fuskanta a lokacin Buhari ne ya haifar da halin da Najeriya ke ciki yanzu.
A cewarsa, Tinubu ba ya mulki don tara kudi ko sayen motoci, sai don gyara kasa da dawo da martabarta da wasu suka lalata.
An tarbi sabon sakataren ADC a Legas
A wani rahoton, kun ji cewa Sakataren hadakar ADC, Rauf Aregbesola ya dura jihar Legas bayan fara aiki.
Tsohon gwamnan na Osun ya bayyana cewa za su yi kokarin kawo sauyi a Najeriya idan suka yi nasara.
Aregbesola ya yi kira ga 'yan ADC da su guji zagi ko cin mutuncin wasu jam'iyyu, a maimakon haka ya bukaci su rika tallata tafiyarsu kawai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


