"Allah Ya Taimake Ni": El Rufai Ya Sake Dura kan Gwamnatin Shugaba Tinubu

"Allah Ya Taimake Ni": El Rufai Ya Sake Dura kan Gwamnatin Shugaba Tinubu

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sake yin kalamai kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Malam El-Rufai ya bayyana cewa saɓanin abin da ake tunani bai taɓa kasancewa na kusa da Tinubu ba a siyasance
  • Babban 'dan siyasar ya nuna cewa Allah ne ya kiyaye shi daga shan kunya shiyasa bai tsinci kansa a gwamnatin Tinubu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sake yin magana kan dangantakarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Malam Nasir El-Rufai ya kuma bayyana nadamarsa kan goyon bayan Shugaba Tinubu ya hau kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

El-Rufai ya caccaki Shugaba Tinubu
El-Rufai ya soki gwamnatin Shugaba Tinubu Hoto: @elrufai, @DOlusegun
Source: Twitter

Tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Prime Time' na tashar Arise Tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me El-Rufai ya ce kan gwamnatin Tinubu?

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya fadi shirinsa don kifar da Shugaba Tinubu a 2027

El-Rufai ya bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin "annoba" da ya gode wa Allah da bai shiga cikinta ba.

Tsohon gwamnan ya bayyana yadda gwamnonin Arewa na jam’iyyar APC suka yanke shawarar miƙa mulki zuwa Kudu bayan ƙarewar wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda hakan ya buɗe hanyar da Tinubu ya hau mulki.

“A gare mu a matsayinmu na gwamnonin Arewa na APC, mun ji cewa bayan shekaru takwas na mulkin Buhari, kamata ya yi mulki ya koma Kudu."
"Tambaya ta biyu ita ce wa zai iya cin zaɓe daga jam’iyyar? Bola Ahmed Tinubu ne ya ci gajiyar hakan."

- Nasir El- Rufai

El-Rufai ya ƙara da cewa, akasin abin da jama’a ke zato, bai taɓa kasancewa kusa da Tinubu a siyasance ba.

"Ba na kusa da Bola Tinubu. Ni na kasance yaron Buhari ne, shi kuma Tinubu yana da nasa yaran. Ni na wajen Buhari ne. Aiki na shi ne na tabbatar Kaduna ta ba Tinubu ƙuri’u lokacin da ya lashe tikitin takara na jam’iyya."

Kara karanta wannan

An jefi Shugaba Tinubu yayin ziyara a Kaduna? An ji yadda lamarin ya kaya

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya bayyana cewa yana da kyakkyawan fatan cewa Tinubu zai zaɓi ƙwararru a matsayin ministoci, amma hakan bai faru ba.

"Abin da nake da kusan tabbaci a kai shi ne, Tinubu zai zaɓi ƙwararru a majalisar ministocinsa. Amma babu inganci."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya yi kalamai kan gwamnatin Tinubu
El-Rufai ya ce Allah ya tsare.shi daga shiga gwamnatin Tinubu Hoto: @elrufai
Source: Twitter

El-Rufai ya ƙi karɓar tayin Tinubu

Ya kuma bayyana cewa ya ƙi amincewa da tayin da Tinubu ya masa na shiga gwamnatinsa, kuma yanzu yana jin cewa hakan ya tabbatar da cewa ya yi daidai.

“Ina ganin Allah ne ya tsare ni daga shan kunyar wannan masifar. Tinubu ya roƙe ni a bainar jama’a da na yi aiki a gwamnatinsa, akwai bidiyoyin."
"Ta yaya za su ce ya roƙe ni kan na canza shirina? Na gode wa Allah, domin bana da buƙatar na riƙa ba wa ƴan Najeriya amsa kan rashin wutar lantarki da kashe-kashe."

- Nasir El-Rufai

Tinubu ya caccaki gwamnatin El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya caccaki tsohuwar gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya taso masu sukar Tinubu a gaba, ya fadi kuskurensu

Mai girma Bola Tinubu ya bayyana tsohuwar gwamnatin a matsayin ta danniya da rashin tausayin jama'a.

Shugaban ƙasan ya kuma yabawa Gwamna Uba Sani kan irin sauyin da ya kawo a Kaduna tun bayan ɗarewarsa kan kujerar mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng