Rikicin Rivers: Yadda Gwamna Fubara Ya Tsuguna a gaban Wike Ya Nemi Gafara
- Gwamna Siminalayi Fubara ya kai ziyara gidan tsohon ubangidansa Nyesom Wike domin neman yafiya da daidaita tsakaninsu
- Ziyarar ta biyo bayan ganawa da Simi Fubara ya yi da shugaban kasa Bola Tinubu a London kan rikicin siyasar Jihar Ribas
- Rahotanni sun ce gwamna Dapo Abiodun da tsohon gwamna Olusegun Osoba ne suka raka Fubara har gida inda ya roƙi Wike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Rahotanni na nuni da cewa gwamnan jihar Ribas da ke Kudu maso Kudancin Najeriya, Siminalayi Fubara, ya kai wata muhimmiyar ziyara gidan Nyesom Wike.
Bayanai da suka fito sun nuna cewa Fubara ya kai ziyarar ne domin neman gafara da sulhu kan rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa ziyarar ta faru ne kwanaki bayan Fubara ya gana Bola Ahmed Tinubu a birnin London, inda suka tattauna kan rikicin siyasar Ribas.

Kara karanta wannan
Atiku ko Obi?: El Rufa'i ya yi magana kan tsayar da 'dan takaran 'yan adawa a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta shaida cewa Fubara ya je gidan Wike ne tare da rakiyar gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, da kuma tsohon gwamnan jihar, Olusegun Osoba.
A wajen ganawar, Siminalayi Fubara ya rusuna har ƙasa yana rokon Wike tare da kiran sa “Oga na”.
Fubara ya rusuna ya na neman gafarar Wike
Ganawar ta gudana ne a ranar Juma’a, 18 ga Afrilu, a gidan Wike da ke Abuja, kuma rahotanni sun ce Fubara ya zauna har zuwa safiyar ranar Asabar, 19 ga Afrilu.
A cewar majiyar, Fubara ya kama ƙafafun Wike yana mai kiran sa da kalmar “Oga na”, a cikin halin roƙo da neman gafara.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken abin da suka tattauna ba, domin wasu daga cikin wadanda ke da masaniya da batun sun ƙi yin magana da 'yan jarida.
Amma rahotanni sun ce an bukaci Fubara da ya taro magoya bayansa da dattawan jihar ya bayyana musu gaskiyar abin da ke faruwa tsakaninsa da Wike.
An tabbatar da ganawar Fubara da Wike
PM News ta rahoto cewa Mai magana da yawun Wike, Lere Olayinka, ya tabbatar da cewa ganawar ta gudana, amma ya ce bai san abin da suka tattauna ba.
Haka zalika, mai magana da yawun Fubara, Nelson Chukwudi, ya ce ba zai yi magana kan batun ba, yana mai tura tambayoyi zuwa ofishin kwamishinan yada labarai na jihar Ribas.
Yayin da manema labarai suka tuntubi kwamishinan yada labaran, bai amsa kiran da aka masa har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Asalin rikicin Fubara da Wike a Rivers
Rikicin siyasar Ribas ya fara ne kimanin wata shida bayan Fubara ya karbi mulki daga hannun Wike a shekarar 2023.
Rikicin ya raba majalisar dokokin jihar gida biyu – yan majalisa 27 na biyayya ga Wike, yayin da uku suka tsaya tare da Fubara.

Source: Instagram
Fubara ya ki amincewa da sauran yan majalisar bisa dalilin cewa sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, kuma hakan ya sa suka rasa kujerunsu.
Haka rikici ya cigaba da gudana a jihar har ya kai ga dakatar da gwamna Siminalayi Fubara a watan Maris.
Ana rade radin Fubara zai koma APC
A wani rahoton, kun ji cewa ana rade radin gwamna Siminalayi Fubara zai iya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Rahotanni sun nuna cewa jita jitar ta fara karfi ne bayan Siminalayi Fubara ya gana da Bola Tinubu a London.
Ana ganin cewa sauya shekar gwamna Simi Fubara zuwa jam'iyyar APC mai mulki zai iya kawo karshen rikicin siyasar jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

