‘Yan Autan Gwamnonin Jihohi da Aka Yi a Najeriya Tun Daga Zaben 1999 Zuwa 2023

‘Yan Autan Gwamnonin Jihohi da Aka Yi a Najeriya Tun Daga Zaben 1999 Zuwa 2023

Abuja - Ana yawan kukan cewa ya kamata a ba matasa damar rike madafan ido a Najeriya, a lokutan baya irin haka ta faru.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Akwai lokacin da aka rika samun matasa masu shekaru kasa da 40 da aka zaba a kan mulki, kuma suka zama gwamnonin jihohi.

A rahoton nan, mun kawo sunayen ‘yan autan gwamnonin da aka yi daga lokacin da aka dawo mulkin farar hula a 1999 zuwa 2024.

‘Yan Autan Gwamnoni
Wadanda suka zama Gwamnoni a kananan shekaru a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wadanda suka zama Gwamnoni a kananan shekaru

1. Ibrahim Saminu Turaki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Statisense ta wallafa cewa Alhaji Ibrahim Saminu Turaki ya zama gwamnan Jigawa yana mai shekara 35 da kwanaki 328 a duniya.

Kara karanta wannan

Sojan da aka fafata a juyin mulkin 1966 a Najeriya da shi ya rasu a yau

Saminu Turaki ya yi mulki na shekaru takwas a jere daga 1999 zuwa 2007, ya kuma yi zarra sosai a bangaren ilmin ICT na zamani.

2. Donald Duke

A lokacin da Mista Donald Duke ya zama gwamna a jihar Kuros Riba a Mayun 1999, shekarunsa 37 da kwanaki 250 cif a doron kasa.

A shekarun kuruciya shakaf Duke ya yi mulki a Kalaba. Idan za a tuna, a zamaninsa jihar Kuros Riba ta yi fice wajen zuwa yawon bude ido.

3. Ahmad Sani Yariman-Bakura

Mutanen Zamfara sun zabi Ahmed Sani Yeriman Bakura a matsayin gwamnansu na farko a tarihi yana shekara 378 da kwanaki 320 a duniya.

Har ya sauka daga mulki shekarunsa 46, hakan ya ba shi damar daukar shekaru a majalisar dattawa, ya jaddada shari’ar musulunci a mulkinsa.

4. Chimaroke Nnamani

Dr. Chimaroke Nnamani ya dare kujerar gwamna a jihar Enugu yana mai shekaru 39 da kwanaki 8 a ranar karshe na watan Mayun 1999.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin gwamnoni da basu ga maciji da yaran gidansu bayan ɗarewa mulki

Fitaccen ‘dan siyasar wanda ya rika yamutsa hazo gabanin zaben 2023 a PDP. Har gobe dai ana damawa da Nnamani a fagen siyasa.

5. Orji Uzor Kalu

Wani tsohon gwamna daga Kudu maso gabas da yake cikin jerin nan shi ne Orji Uzor Kalu da ya shiga ofis a shekara 39 da kwanaki 47.

Kafin ya cika shekara 40 a duniya aka rantsar da Orji Uzor Kalu a mulki. Shekaru bayan barinsa mulki, shi ma ya shiga gidan yari.

Dokar kashe barayin gwamnati

Idan Injiniya Muazu Magaji ya samu yadda yake so, ana da labari cewa barayin gwamnati a Najeriya ba za su kwana a duniya ba.

Dan sarauniya ya ce yadda ake neman yakar masu harkar kwayoyi, a bi masu sace kudin gwamnati ganin an taso masu safarar kwaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel