Jam'iyyar SDP ta bayyana matsayar ta kan kwace takarar Duke da kotu tayi
- Jam'iyyar SDP ta ce ba za ta fifita kowa cikin 'yan takarar shugabancin kasar ta ke fafatawa a kotu ba
- SDP ta ce dukkan su goggagun 'yan siyasa ne masu basira da za su iya kai Najeriya ga tudun na tsira idan suyi nasara
- Jam'iyyar kuma tayi kira da 'ya'yan ta su cigaba da yakin neman zabe sannan su guji aikata abinda zai kawo rabuwar kai tsakaninsu
Shugaban jam'iyyar Social Democratic Party, SDP ya ce jam'iyyar ba za ta nuna fifiko ga kowanne dan takarar ba a shari'ar da aka gwabzawa tsakanin Farfesa Jerry Gana da tsohon gwamnan jihar Cross Rivers, Donald Duke a kan kujerar takarar shugabancin kasar jam'iyyar a zaben 2019.
Jam'iyyar ta ce dukkan 'yan takarar biyu goggagun 'yan siyasa ne da za su iya kai jam'iyyar ga nasara.
Jam'iyyar ta bayar wannan sanarwan ne cikin wani sako da ta baiwa manema labarai jiya a Abuja ta bakin sakateren watsa labarai na jam'iyyar, Alhaji Alfa Mohammed a yayin da ta ke fadin matsayar ta kan hukuncin kotun da cewa Jerry Gana ne dan takara na asali.
DUBA WANNAN: Cikaken jerin sunayen mambobin majalisar wakilai da ba za su koma majalisar ba a 2019
Sanarwar ta ce, "Jam'iyyar mu tayi ammana cewa dukkan 'yan takarar biyu goggagun 'yan siyasa ne da ke biyaya ga jam'iyya kuma suna da basira da za su iya gai Najeriya ga tudun na tsira.
"SDP ta kuma amince da cewa dukkan dan Najeriya yana da ikon zuwa kotu domin a bi masa hakkinsa kamar yadda Farfesa Jerry Gana ya yi kuma shine Donald Duke yana da damar ya daukaka kara kamar yada ya yi alkawarin zai yi.
"Duk da cewa jam'iyyar ba ta da gwani a tsakanin 'yan takarar biyu, ta ce a shirye ta ke ta bayyana a kotu domin kare kanta bisa zaben fidda gwani da ta gudanar."
Jam'iyyar kuma tayi kira ga dukkan 'ya'yan ta su cigaba da yakin neman zabensu kamar yada suka fara kuma su guji aikata duk wani abu da zai iya haifar da rabuwan kai tsakanin 'ya'yan jam'iyyar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng