Orji Uzor-Kalu: Ba na kunyar zuwa kurkuku, Allah ne ya kaddara hakan

Orji Uzor-Kalu: Ba na kunyar zuwa kurkuku, Allah ne ya kaddara hakan

- Sanata Orji Uzor-Kalu ya bayyana cewa shiga gidan yari wani abu ne da ya canza masa rayuwa

- Tsohon gwamnan na jihar Abia ya ce yana daga cikin kaddararsa shafe wani lokaci a gidan yari

- Kalu yana mayar da martani ne game da kalaman abokan hamayyarsa na siyasa da suke yi masa ba'a kan tsare shi na wata 6

Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa ba ya jin kunyar zaman watanni shida da yayi a kurkuku.

Kalu wanda shine sanata mai wakiltar yankin Abia ta Arewa a yanzu ya yi wannan tsokaci ne a wurin kamfen din Mascot Uzor Kalu, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a mazabar Aba ta Arewa / ta Kudu a majalisar wakilai.

Mascot kani ne ga Orji, wanda kuma shi ne babban bulaliyar Majalisar Dattawan Najeriya a halin yanzu.

Orji Uzor-Kalu: Ba na kunyar zuwa kurkuku, Allah ne ya kaddara hakan
Orji Uzor-Kalu: Ba na kunyar zuwa kurkuku, Allah ne ya kaddara hakan
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fitaccen dan siyasar PDP a Kudu maso Yamma ya mutu a hatsarin mota

Sanatan yana mayar da martani ne ga kalaman da aka alakanta da Gwamna Okezie Ikpeazu da Sanata Enyinnaya Abaribe, shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa.

Kwanaki mutanen biyu sun yi wa Kalu ba’a inda suka ce bai farfado daga halin da ya shiga a gidan yari ba bayan da ya tabbatar da cewa hanyoyin da ke Abia gwamnatin tarayya ce ta biya su ko kuma hukumar ci gaban Neja Delta.

Jaridar The Cable ta ruwaito Kalu yana cewa:

“Yanzu karfe 10 na dare kuma ina nan tare da ku, shin gwamna ko Abaribe za su iya zuwa nan? Wannan shine dalilin da ya sa a jagoranci, dole ne ka kasance tare da mutanen da kake jagoranta.

“Amma ba su fahimci wannan fasaha mai sauki ba, duk ayyukan da suke ikirarin suna yi duk a rediyo suke, ba komai a kasa. Annabi Yusuf ya shiga kurkuku, hatta Obasanjo ma ya shiga kurkuku.

"Zuwa gidan yari wani bangare ne na rubutun rayuwata kuma ina godiya ga Allah da ya yarda da hakan."

KU KARANTA KUMA: Bidiyon Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yana nuna kwarewarsa a harkar rawa

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mai magana da yawun gwamna Ikpeazu, Mista Onyebuchi Ememanka, ya caccaki Kalu kan ikirarin da ya yi na cewa gwamnatin tarayya ce ke daukar nauyin aikin titin Aba ta hanyar tallafinta.

Ememanka ya ce babu kamshin gaskiya a cikin ikirarin na Kalu, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar ce ke daukar nauyin ayyukan da ke gudana a Aba.

A wani labarin, Salihu Yakasai (wanda aka fi sani da Ɗawisu), tsohon mai taimakawa gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa bazai yuwu abar makiyaya suna kiwo a buɗe ba, wajibi ne a hana su.

Yakasai ya faɗi wannan magana ne ya yin da yake maida martani kan wani bidiyo da aka saki a kafar sada zumunta.

Bidiyon ya nuna wata mata a jihar Ogun na kuka saboda shanu sun shiga gonar kayan lambun ta suna kiyo, su kuma fulanin dake kiwon sun tsaya suna kallo.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit

Online view pixel