LABARI DA DUMI DUMI: An saki tsohon gwamnan jihar Jigawa daga gidan kaso

LABARI DA DUMI DUMI: An saki tsohon gwamnan jihar Jigawa daga gidan kaso

- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarnin sake tsahon gwamnan jihar Jigawa daga gidan yari

- Saminu Turaki ya yi fiye da makonin biyu a gidan yari

- Babbar kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 28 ga watan Satumba

Babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja ta ba da umarnin saki tsohon gwamnan jihar Jigawa, Ibrahim Saminu Turaki a safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli daga gidan kaso bayan da ya shafa fiye da makonni biyu a rufe.

Tsohon gwamnan ya kasance a gidan yari da ke Kuje a Abuja fiye da mako guda duk da cewa ya cika sharudan belinsa.

idan ba a manta ba, hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta cafke Turaki a ranar 4 ga watan Yuli a wata taron kaddamar da wani littafin a Abuja yayin da hukumar ta tsare shi.

LABARI DA DUMI DUMI: An saki tsohon gwamnan jihar Jigawa daga gidan kaso
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Ibrahim Saminu Turaki

A ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli 2017, Justice Yusuf Halilu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya ba da belin tsahon gwamnan, amma hukumar ta yi tir da yin haka inda ta ci gaba da tsare shi ko da bayan ya cika sharudan belin.

KU KARANTA: Masu gudu su gudu! EFCC ta bankado badakalar N329 biliyan tsakanin kamfunnan mai da NNPC

Legit.ng ta ruwato cewa lauyoyin Saminu Turaki sun yi karar shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu a babbar kotun tarayya da ke Abuja. Kotun ta saurari karar a ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli 2017 yayin da ta dage sauraren karar zuwa ranar 28 ga watan Satumba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel